Nigerian news All categories All tags
Zaben 2019: Za mu kawo maka Jihar Kogi - Gwamna Bello ya fadawa Buhari

Zaben 2019: Za mu kawo maka Jihar Kogi - Gwamna Bello ya fadawa Buhari

- Gwamna Yahaya Bello yace Shugaba Buhari ya amsa kiran su

- Gwamnan ya ji dadi da ya ga Shugaban kasar zai nemi tazarce

- Bello yace su na tare da Shugaban kasa Buhari a zaben na 2019

Mun samu labari cewa Gwamna Yahaya Bello na Jihar Kogi yayi farin cikin jin cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai nemi takara a 2019. Gwamnan yace za su ba Shugaban goyon-bayan da ya dace.

Zaben 2019: Za mu kawo maka Jihar Kogi - Gwamna Bello ya fadawa Buhari

Gwamnan Kogi yace za su yi Shugaba Muhammadu Buhari a 2019

Darekta-Janar na yada labaran Gwamnatin Jihar Kogi Kingsley Fanwo ya bayyana cewa Gwamna Yahaya Bello a shirye yake da ya kira Jama’ar Jihar sa da su fito su sake zaben Shugaban kasa Buhari a zabe mai zuwa na 2019.

KU KARANTA: Zan iya fadawa wuta saboda Shugaba Buhari - Gwamnan Kogi

Gwamnan ya bayyana cewa shi fa ‘dan-a-mutun Shugaba Buhari ne kuma duk inda Shugaban ya sa kafa yana nan. Yahaya Bello yace mutanen Jihar Kogi ne su ka fara kiran Shugaban kasa Buhari ya nemi tazarce a zabe mai zuwa.

Yahaya Bello ya nuna godiyan sa ga Shugaba Buhari da ya ji rokon su na sake fitowa takara inda yace su na tare da tsare-tsaren sa na yaki da barna da kuma habaka tattali da inganta harkar tsaro ya kuma yi kira APC ta kara hada kai.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel