Nigerian news All categories All tags
Manyan ‘Yan siyasan da su ka ji dadin cewa Buhari zai nemi tazarce a 2019

Manyan ‘Yan siyasan da su ka ji dadin cewa Buhari zai nemi tazarce a 2019

Wasu Gwamnoni sun nuna farin cikin su da jin cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai nemi ya zarce a zaben 2019. Daga cikin wadannan Gwamnoni akwai:

Manyan ‘Yan siyasan da su ka ji dadin cewa Buhari zai nemi tazarce a 2019

Wasu Gwamnoni sun ji dadin jin labarin tazarcen Buhari

1. Nasir El-Rufai

Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ne ya fara bayyanawa Duniya cewa Shugaban kasar zai sake neman takara a 2019 inda ya fito cikin murna yana nuna goyon bayan wannan mataki da Shugaban kasar ya dauka.

2. Yahaya Bello

Gwamna Yahaya Bello ya nuna jin dadin sa bayan ya ji cewa Shugaba Buhari zai nemi zarcewa inda yace a shirye yake ya kira Jama’ar Jihar sa da su fito su sake zaben Shugaba Buhari a zabe mai zuwa na 2019 idan ya zo.

KU KARANTA: Matsin lamba ya sa Buhari ya bayyana aniyar sa - Shettima

3. Aminu Masari

Gwamnan Jihar Katsina inda Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fito yayi farin cikin jin cewa Shugaban kasar zai fito takara kuma a zabe mai zuwa. Gwamnan dama a baya yace duk mai son kasar nan zai zabi Buhari a 2019.

4. Rochas Okorocha

Gwamnan Jihar Imo mai shirin barin gado a 2019 ya nuna farin cikin sa da jin cewa Shugaban kasa Buhari zai nemi tazarce a zabe na gaba. Ba mamaki Gwamnan ya nemi takarar Shugaban kasa a zaben 2023 idan ya zagayo.

5. Abubakar Sani Bello

Gwamnan Neja watau Abubakar Sani Bello ya bayyana cewa sun yi farin ciki matuka da jin cewa Shugaba Buhari zai fito takara a zabe mai zuwa. Gwamnan na APC yace wannan abu da su ka ji jiya a taron Jam’iyya yayi masu dadi kwarai.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel