Nigerian news All categories All tags
Hukumar EFCC ta damke wani da kudi $400,000 na bogi

Hukumar EFCC ta damke wani da kudi $400,000 na bogi

Hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa a ranan Asabar, 7 ga watan Afrilu ta damke wani dan damfara mai suna, Samson Otuedon, a unguwar Masaka, karamar hukumar Karun a jihar Nasarawa.

Samson ya kware wajen hada kudaden bogi ya kasance yana damfaran jama’a. hukumar ta samu labara akanshi ne rana Juma’a, 6 ga watan Afrilu kawai sai ta far mas aba tare da bata lokaci ba.

Hukumar EFCC ta damke wani da kudi $400,000 na bogi

Hukumar EFCC ta damke wani da kudi $400,000 na bogi

An damke shi da sabbin kudade akalla $400,000 (Dala dubu dari hudu). Yayinda ake gudanar da bincike akansa, ya bayyana cewa wasu abokan aikinshi da ke Legas ne suka bashi kudin.

Hukumar ta bayyana cewa za ta gurfanar da shi muddin an kamala bincike.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a: https://facebook.com/naijcomhausa https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel