Nigerian news All categories All tags
Shugaba Buhari ya musanta amincewa da kashe biliyan $1 domin sayen kayan aiki ga sojin Najeriya

Shugaba Buhari ya musanta amincewa da kashe biliyan $1 domin sayen kayan aiki ga sojin Najeriya

- Shugaba Muhammadu Buhari ya musanta cewar ya amince da kashe Dalar Amurka biliyan $1 domin sayen makamai ga sojin Najeriya

- A ranar laraba, 4 ga watan Afrilu, Ministan tsaro, Mansur Ali, ya bayyana cewar shugaba Buhari ya saki adadin kudin

- Shugaba Buhari, ta bakin mai taimaka masa na musamman, Sanata Ita Enang, ya ce har yanzu maganar kudin na bin matakan da suka dace tukunna

A yau, Litinin, 9 ga watan Afrilu, shugaba Buhari ya musanta cewar ya ware Dalar Amurka biliyan $1 domin sayen makamai ga sojin Najeriya.

A ranar Laraba, 4 ga watan Afrilu, jaridar Daily Trust ta rawaito ministan tsaro, Mansur Dan-Ali, na cewar shugaba Buhari ya ware adadin kudin domin sayen makamai ga hukumar sojin Najeriya.

Shugaba Buhari ya musanta amincewa da kashe biliyan $1 domin sayen kayan aiki ga sojin Najeriya

Shugaba Buhari

Batun amincewa da kashe kudin ya jawo korafi daga bangaren majisar kasa da suka ce ba a tuntube su ba.

A jiya ne shugaban majalisar dattijai, Sanata Abubakar Bukola Saraki, ya bayyanawa duniya cewar shugaba Buhari bai tuntubi shugabancin majalisar tarayya ba kafin ya amince da fitar da dala biliyan $1bn daga asusun kasa domin sayen kayan aiki ga hukumar sojin Najeriya ba.

DUBA WANNAN: Buhari ya yi gaban kansa ne kawi a batun fitar da biliyan $1bn - Saraki

Saidai a yau, Litinin, shugaba Buhari, ta bakin mai bashi shawara a kan majalisar dattijai, Sanata Ita Enang, ya ce har yanzu maganar ware kudin na bin matakan da suka dace tare da bayyana cewar har yanzu ba a kai ga matakin amincewar shugaba Buhari ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel