'Yan daba sun tafka barna a ofishin yakin neman zaben Atiku, kalli hotunan ta'adin da suka yi
Wasu matasa da ake zargin 'yan sara-suka ne sun kai farmaki ofishin yakin neman zaben Atiku dake kan titin Dandagoro a garin Katsina tare da lalata motocin dake harabar ofishin.
'Yan dabar sun kai farmakin ne a karshen mako kuma sun rufe jama'ar dake ofishin da duka.
Jacob Dickson, kakakin kungiyar yakin neman zaben Atiku shiyyar Arewa maso yamma ya ce, 'yan dabar sun lalata dukiyar miliyoyin Naira yayin farmakin da suka kai.
Aliyu Abbas, shugaban wata kungiyar magoya bayan Atiku a jihar ya bayyana abinda matasan suka aikata da cewar ta'addanci ne a kan jama'ar dake ofishin.
DUBA WANNAN: Matsin lamba ya saka Buhari bayyana kara tsayawa takara - Gwamna Shettima
Wani shaidar gani da ido ya ce, 'yan dabar sun zo ne cikin babura masu kafa uku guda uku sun fara ganin abinda ke faruwa a ofishin kafin daga bisani su kawo farmakin.
Magoya bayan Atiku a jihar na zargin cewar 'yan dabar sun kawo masu harin ne saboda a ofishin aka yi taron gangamin jam'iyyar PDP na shiyyar arewa maso yamma.
Magoya bayan Atikun sun ce sun sanar da ofishin 'yan sanda na Batagarawa abinda ya faru kuma tuni hukuma ta fara binciken lamarin.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng