Siyasa: Mafarkin Ganduje na Baiwa Buhari kuri'a miliyan 5 na shirin zama gaskiya
- Matasan Kano suna cikin farin ciki
- A cewarsu, ba sa son wani ya hau don kar yayi fatali da aiyukan da Buharin ya fara
- Wasu kuma sun ce, tsoronsu shi ne kar wani yayi awon gaba da kudaden da Buharin ya kwato a wajen barayi
Amincewar Shugaba Muhammadu Buhari ya fito takara a 2019, ya sanya matasan Jihar Kano murna da shewa.
A cewar matasan dai, su na mutukar murna sakamakon amince da Buhari yayi ya tsaya takara, a yau Litinin a shelkwatar jam’iyyar dake Abuja.
Jihar Kano dai ita ce babbar cibiyar soyayya da goyon bayan siyasar Buhari, tun daga lokacin da ya fara fitowa takara a 2003 da 2007 da 2011 har ya zuwa lokacin da ya samu nasara a 2015.
Wasu daga cikin matasan da wakilimnu ya zanta da su, sun shaida masa cewa, sai yanzu suka samu kwarin gwuiwa da nutsuwa, sakamakon Shugaba Buhari zai samu damar karasa duk aiyukan da ya faro na cigaban kasa, idan har ya zarce a zaben 2019. A cewar jaridar Daily Nigerian
wani matashi mai suna Usman Baba, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN), cewa, shekaru uku da shugaba Muhammadu Buhari yayi, yana mulki ya mayar da hankali ne kan yakar cin-hanci da rashawa da ya addabi Najeriya ne.
“ Mun yi murna sosai, sanan muna fata Buhari zai sake zarcewa don mayar da hankali wajen aikace-aikacen gina kasa, don tunda ya hau mulki yake yaki da barayi.” Baba ya fada.
Usman ya cigaba da cewa, “Ba ma son wani ya zo ya barnatar da kudaden da aka kwato daga hannun barayi, shi yasa muke son shi Buharin ya dora”
KU KARANTA: Mutane 5 da suka sanya Buhari ya sake tsayawa takara a zaben 2019
Dama dai a watan Faburairu ne, Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya yiwa Shugaba Buhari alkawarin kuri’a miliyan biyar (5m) don taimaka masa sake zarcewa a 2019.
Haka zalika a cikin watan nan na Afrilu ne Gwamanan yayi ikirarin karar Shugaba Baharin, mutukar yaki yarda yayi takara a 2019.
Wata mata mai suna Malama Maryam Musa, ta bayyana nata ra’ayin da cewa, tabbas duniya tayi na’am da Buhari a matsayin shugaba mai amana da kuma tsantseni.
In dai ba’a manta ba, a gaba daya kuri’un da aka kada a Kano a zaben 2015, sun kai har 2,172,447, kuma Shugaba Muhammadu Buhari ya samu nasarar samun 1,903,999 yayin da ragowar jam’iyyun suka samu 250,000 kacal. Wanda hakan yake nuni da irin farin jinin da yake da shi a tsakanin al’umma.
Abdullahi Umar Ganduje, wanda shi ne Gwamnan na Kano, masoyi ne babba na shugaba Buhari, a dalilin hakan yasa lokacin da yake jiyya a birnin London ya shirya aka yi masa addu’a a gidan gwamnati, kana da ya dawo Najeriya ya sanya aka shirya gagarumin taro don murnar dawowarsa watan Augusta 2017.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng