Nigerian news All categories All tags
Matsin lamba ya saka Buhari bayyana kara tsayawa takara - Gwamna Shettima

Matsin lamba ya saka Buhari bayyana kara tsayawa takara - Gwamna Shettima

Gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima, ya bayyana cewar matsin lamba ya saka shugaba Buhari bayyana kara tsayawa takarar shugaban kasa a yau, Litinin.

Shettima ya bayyana hakan ne yayin ganawa da manema labarai a yau, jima kadan bayan ganawar sa da shugaban ma'aikatar fadar shugaban kasa, Abba Kyari, a fadar gwamnati, Villa.

Matsin lamba ya saka Buhari bayyana kara tsayawa takara - Gwamna Shettima

Buhari da Shettima

Da yake amsa tambayar ko Buhari ya tuntubi gwamnonin jam'iyyar APC kafin bayyana niyyar sa ta sake yin takarar, Shettima ya bayyana cewar, babu wata doka ko yarjejeniyar sai ya sanar da gwamnoni kafin ya bayyana niyyar sa ta sake yin takarar.

DUBA WANNAN: Gida da ofishin shugaban kasar Amurka sun yi gobara

Kazalika, gwamnan ya bayyana cewar, hankalin jam'iyyar zai kwanta tunda Buhari ya fito karara ya bayyana cewar zai sake tsayawa takara.

Shettima ya kara da cewar dukkan gwamnonin jam'iyyar APC na goyon bayan takarar shugaba Buhari tare da bayyana cewar zasu bashi gudunmawa tamkar yadda suka bashi a zaben 2015.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel