Nigerian news All categories All tags
Yanzu-yanzu: Shugaba Muhammadu Buhari ya tafi Ingila

Yanzu-yanzu: Shugaba Muhammadu Buhari ya tafi Ingila

Shugaban kasan Najeriya, Muhammadu Buhari, ya tafi kasan Birtaniya a yau Litinin, 9 ga watan Afrilu 2018.

Jirgin shugaban kasan ya tashi ne da yammacin nan ga da lokacin la’asar a babban filin jirgin saman Nnamdi Azikwe da birnin tarayya Abuja.

Shugaba Buhari ya tafi Birtaniya ne domin ganawa da Firam ministan Ingila, Theresa May, domn tattauna al’amuran diflomasiyya tsakanin Najeriya da Birtaniya.

Bayan haka, zai garzaya taron shugabannin kasashe mambobin Commonwealth da za’ayi tsakanin 18 ga 20 watan Afrilu, 2018.

Yanzu-yanzu: Shugaba Muhammadu Buhari ya tafi Ingila

Yanzu-yanzu: Shugaba Muhammadu Buhari ya tafi Ingila

Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa shugaba Buhari ya alanta niyyar sake takara zaben kujeran shugaban kasan Najeriya a shekarar 2019.

KU KARANTA: Na amsa kiran yan Najeriya ne – Shugaba Buhari

Shugaban kasan ya bayyana wannan ne a taron masu ruwa da tsaki a jam’iyyar da aka gudanar yau Litinin, 8 ga watan Afrilu, 2018 a sakataiyar jam’iyyar da ke babban birnin tarayya, Abuja.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a: https://facebook.com/naijcomhausa https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel