Nigerian news All categories All tags
Yarinyar da ake cewa mayya saboda lankwasassun kafafuwanta ta samu anyi mata aiki kyauta a kafar ta gyaru

Yarinyar da ake cewa mayya saboda lankwasassun kafafuwanta ta samu anyi mata aiki kyauta a kafar ta gyaru

- Wata matashiya wadda ake cewa mayya saboda lankwasassun kafafuwanta ta samu anyi mata aiki kyauta an tayar da kafafuwan

- Yarinyar mai suna Julienne ‘yar kasar Kamaru ce wadda tun tana jaririya mahaifiyarta, Veronique taga alamun lankwasar kafafuwan yarinyar

- Kungiyar bayardatallafi kyauta ta Mercy Ships ta dauki nauyin yiwa Julienne aiki kyauta, don su gyara mata rayuwarta

Wata matashiya wadda ake cewa mayya saboda lankwasassun kafafuwanta ta samu anyi mata aiki kyauta, an tayar da kafafuwan su mike kamar yanda na sauran mutane suke.

Yarinyar mai suna Julienne, ‘yar kasar Kamaru ce, wadda tun tana jaririya mahaifiyarta, Veronique taga alamun lankwasar kafafuwan yarinyar.

Yarinyar da ake cewa mayya saboda lankwasassun kafafuwanta ta samu anyi mata aiki kyauta a kafar ta gyaru

Yarinyar da ake cewa mayya saboda lankwasassun kafafuwanta ta samu anyi mata aiki kyauta a kafar ta gyaru

Julianne ta bayyana yanda ta ringa shan wahalar zuwa makaranta a lokacin, cikin zafin rana da komai, duk da cewa bayan anyi aikin ma, sunsha fama da likitan kashi Meg Crameri kafin ya samu ta fara tafiya, sannan har ya amince cewa tana iya komawa gida wurin iyayenta.

KU KARANTA KUMA: Siyasar Sokoto: Tambuwal da Sanata Dahiru sun daidaita tsakaninsu

Kungiyar bayardatallafi kyauta ta Mercy Ships ta dauki nauyin yiwa Julienne aiki kyauta, don su gyara mata rayuwarta, sakamakon danginta bazasu iya daukar nauyin aikin da akace da za’ayi mata ba a kasar Ingila.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel