Nigerian news All categories All tags
Gida da ofishin shugaban kasar Amurka sun yi gobara

Gida da ofishin shugaban kasar Amurka sun yi gobara

Rahotanni daga birnin New York sun tabbatar da cewar mutum guda ya mutu sakamakon tashin gobara a ofishi mai hade da gida na shugaban kasar Amurka, Donald Trump.

Gobarar ta tashi ne a hawa na hamsin a ginin ofishin mai hade da gida da ake kira Trump tower dake birnin New York ta kasar Amurka.

Gida da ofishin shugaban kasar Amurka sun yi gobara

Gida da ofishin shugaban kasar Amurka sun yi gobara

Hukumar kashe gobara ce ta ceto mutumin mai shekaru 67 daga cikin ginin kafin daga bisani ya mutu a asibiti.

DUBA WANNAN: Buhari ya yi gaban kansa ne kawi a batun fitar da biliyan $1bn - Saraki

Jami'an hukumar kashe gobara 200 ne suka yi aikin kashe gobarar. Hudu daga cikinsu sun samu raunuka. Kazalika an takaita zirga-zirgan ababen hawa da mutane yayin kokarin kashe gobarar.

Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya godewa jami'an hukumar kashe gobara bisa nasarar da suka yi na dakatar da gobarar cikin lokaci kankani.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel