Nigerian news All categories All tags
2019: Makarfi, Balarabe Musa sun yi raddi ga burin Buhari na sake tsayawa takarar shugaban kasa

2019: Makarfi, Balarabe Musa sun yi raddi ga burin Buhari na sake tsayawa takarar shugaban kasa

Da dama daga cikin al’ummar Najeriya sun bayyana farin cikinsu game da shawarar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dauka na sake tsayawa takara a shekarar 2019, da nufin yin tazarce har zuwa shekarar 2023.

Sai dai ra’ayi bai zamto daya ba gaba daya, inda tsofaffin gwamnonin jihar Kaduna, Alhaji Balarabe Musa da Sanata Ahmed Muhammad Makarfi sun bayyana cewar sake cin zabe ga shugaba Buhari ba zai zama abin mai sauki ba.

KU KARANTA: Alamu guda 8 a jikin dan Adam dake nuna kamuwa da cutar shanyewar rabin fuska

Musa ya bayyana ma kamfanin dillancin labaru, NAN, cewa suna maraba da shawarar da Buhari ya yanke, amma yace “Ina tabbatar ma yan Najeriya cewa zamu tsayar da dan takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar PRP, wanda zai gwabza da Buhari a zabukan 2019.”

2019: Makarfi, Balarabe Musa sun yi raddi ga burin Buhari na sake tsayawa takarar shugaban kasa

Buhari

A nasa bangaren kuwa, tsohon shugaban jam’iyyar PDP, Makarfi ya bayyana cewar bai yi mamakin matakin da Buhari ya dauka ba, cikin wata wasikar ko ta kwana da ya aiko ma majiyar Legit.ng yana cewa: “Wannan ba wani labari bane, da dai ya fadi akasin haka, sai ace ya zama labari.”

Shi kuwa Kasimu Ciyaman, shugaban kungiyar matasan dadin kowa dake Kwannawa jihar Sakkatwao ya kasa boye farin cikinsa game da shawarar Buharin, inda yace zasu bashi goyon baya dari bisa dari, “don kuwa duk Najeriya babu dan takara kamarsa.” Inji shi.

Hakazalika wata mata mai suna Hajiya Hauwa’u Magode ta gode ma Allah da wannan shawarar da Buhari ya dauka, inda ta yi addu’ar Allah ya yi masa jagora.

A ranar Litinin 9 ga watan Afrilu ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana ma shuwagabannin jam'iyyar APC burinsa na sake tsayawa takara a shekarar 2019.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel