Nigerian news All categories All tags
Dalilai 3 da zasu sanya shugaba Buhari sake takara a zaben 2019

Dalilai 3 da zasu sanya shugaba Buhari sake takara a zaben 2019

- Shugaba Buhari ya yayiwa mutanen jihar Kano rade radin cewa zai sake tsayawa takara a zaben 2019

- Mataimakin shugaban kasa yemi Osinbajo yace ya kamata Buhari ya sake tsayawa takara saboda ya ida cika sauran alkawuran da yayi lokacin kamfen

- Gwamnoni sun matsa akan sai Buhari ya sake tsayawa takara a shekarar 2019

Kamar yadda rahotanni suka kawo, a yau Litinin 9 ga watan Afrilu ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana kudirinsa na sake takara a 2019.

Hakan ya sanya muka duba wasu dalilai da zasu iya samun nasaba da abunda yasa Buharin ya yanke wannan hukunaci.

Shugaba Buhari ya yayiwa mutanen jihar Kano rade radin cewa zai sake tsayawa takara a zaben 2019, ya bayyana hakane a lokacinda yake jawabi a garin Kano a ranar Alhamis.

Shugaba Buhari ya fadawa sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, cewa ba wanda zai iya bata masa suna a idon ‘yan Najeriya akan yanda yake son taimakon talakawan kasar nan, game da alkawuransa da yayiwa talakawan a zaben 2015.

Dalilai 3 da zasu sanya shugaba Buhari sake takara a zaben 2019

Dalilai 3 da zasu sanya shugaba Buhari sake takara a zaben 2019

Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, yace shugaba Muhammadu Buhari yana kokarin cika alkawuran da ya daukarwa ‘yan Najeriya lokacin zabe, sakamakon haka ya kamata su mara masa baya a kan sake zabarsa a 2019 don iyarda wadannan alkawura.

KU KARANTA KUMA: PMB zaiyi takara a 2019 – Karanta sharhin yan Najeriya kan wannan kudiri na Buhari

Gwamnoni sun matsa akan sai Buhari ya sake tsayawa takara a shekarar 2019, inda shi kuma shugaba Buhari yace yana jiran yaji jawabin talakawan Najeriya kafin ya yanke shwara akan tsayawarsa takarar, ya bayyana hakane ga gwamnonin lokacin da suka gabatar masa da kudirinsu a dakin taro na matar shugaban kasa dake fadar shugaban kasar.

Yahaya Bello, gwamnan jihar kogi ya bayyanawa manema labarai cewa, gwamnoni suna bukatar shugaba Buhari ya sake tsayawa takara saboda cigaban da ya kawowa kasar nan, musamman na yaki da cin hanci da rashawa, da kuma rashin tsaro a kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel