Nigerian news All categories All tags
Kudin kasar wajen Najeriya ya tumbatsa cikin watanni 3 a bana

Kudin kasar wajen Najeriya ya tumbatsa cikin watanni 3 a bana

- Kudin kasar wajen Najeriya na ta karuwa a Gwamnatin Buhari

- Yanzu Najeriya ta mallaki sama da Dala Biliyan 46 a asusun ta

- Hakan na bayuwa ne ga wasu tsare-tsare da kuma kasuwar mai

Mun samu labari cewa alkaluma daga babban bankin kasar nan na CBN sun nuna cewa tattalin arzikin kasar nan yana ta habaka kwarai da gaske a mulkin Shugaba Muhammadu Buhari.

Kudin kasar wajen Najeriya ya tumbatsa cikin watanni 3 a bana

Kudin da Najeriya ta tara ba kasar waje ya karu a 2018

A cikin watanni 3 dai kudin da Najeriya ta tara na kasar waje ya karu da kashi 19% bayan da asusun na Najeriya ya karu daga Dala Biliyan 38 a farkon shekarar nan zuwa Dala Biliyan $42 a watan Fubrairu kafin ya karu.

KU KARANTA: Buhari yace zai nemi takarar Shugaban kasa a 2019

Yanzu haka dai da ake magana CBN ta bayyana cewa kudin da Najeriya ta ke da shi a asusun kasar waje ya hauraDala Biliyan 46. An samu haka ne a dalilin hana shigo da wasu kaya cikin kasar da kuma farashin man fetur a Duniya.

Wani babban Jami’in bankin kasar na CBN Isaac Okorafor ya bayyana cewa kudin da Najeriya ta adana a asusun waje ya haura Dala biliyan 46. Yanzu haka bankin kasar na cigaba da kokari wajen ganin Dalar Amurka ba ta yi mugun tashi ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel