Nigerian news All categories All tags
Kwamandojin Sojojin Najeriya dake yaki da yan ta’adda sun ziyarci Sojojin Najeriya dake jinya

Kwamandojin Sojojin Najeriya dake yaki da yan ta’adda sun ziyarci Sojojin Najeriya dake jinya

Babban kwamandan Sojojin Najeriya dake filin daga a jihar Borno, Manjo Janar Nicholas Rogers ya kai ma wasu dakarun Soja dake jinya a garin Maiduguri, a sanadin jikkata da suka yi sakamakon hare haren Boko Haram.

KU KARANTA: Hatsari ba sai a mota ba: Yadda wasu masu hakar ma’adanan kasa suka mutu yayin da kasa ta rufta dasu

Rediyon Sojojin Najeriya ne ta bayyana haka a ranar Litinin 8 ga watan Afrilu, inda tace Kwamandan Rogers ya samu wakilcin mataimakin Kwamanda Commodore Aminu Hassan, tare da wakilin babban kwamandan rundunar ta bakwai dake Borno, Kanal Kasim Sidi, da shugaban ma’aikatan filin daga, Bigediya Idowu Akinlawon da sauransu.

Kwamandojin Sojojin Najeriya dake yaki da yan ta’adda sun ziyarci Sojojin Najeriya dake jinya

Ziyarar

Kwamandojin sun ziyarci cibiyar kula da marasa lafiya dake barikin Sojoji na shelkwata ta 7 dake Maimalari, haka zalika sun leka Sojojin da aka kai su babban asibitin koyarwa na jami’ar Maiduguri.

Rogers ya bayyana cewar sun kai wannan ziyara ne kamar yadda suka saba a kowanni wata, inda suke dubiya ga Sojojinsu, tare da lura da matakin samun warakarsu, haka zalika suna amfani da wannan dama don tabbatar da ingancin kulawar da Sojojinsu ke samu a asibtoci daban daban.

Kwamandojin Sojojin Najeriya dake yaki da yan ta’adda sun ziyarci Sojojin Najeriya dake jinya

Ziyarar

Daga karshe Rogers ya shawarci Sojojin da su jajirce, kuma su rundunar Sojin Najeriya na matukar baiwa samun lafiyarsu muhimmanci, bugu da kari ya yaba ma hukumar asibitin koyarwa ta jami’ar Maiduguri bisa kokarin da suke yi da Sojojinsu.

Kwamandojin Sojojin Najeriya dake yaki da yan ta’adda sun ziyarci Sojojin Najeriya dake jinya

Ziyarar

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel