Nigerian news All categories All tags
Mutanen da Shugaba Buhari ya rikitawa lissafi bayan ya nuna shirin tsayawa takara

Mutanen da Shugaba Buhari ya rikitawa lissafi bayan ya nuna shirin tsayawa takara

Mun samu labari yau Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyanawa Duniya cewa zai nemi takara a 2019. Akwai ‘Yan siyasan da ba mamaki su ke harin kujerar Shugaban kasar kuma za su iya gamuwa da barazana wanda daga cikin su akwai:

Mutanen da Shugaba Buhari ya rikitawa lissafi bayan ya nuna shirin tsayawa takara

Ba mamaki Kwankwaso na shirin tsayawa takara

1. Rabiu Kwankwaso

Tsohon Gwamnan Jihar Kano Sanata Kwankwaso zai gamu da matsala a 2019 idan har Shugaba Buhari zai tsaya takara. Da wuya Kwankwaso ya iya samun tikiti a karkashin Jam’iyyar APC idan har Shugaba Buhari yana kan mulki.

KU KARANTA: Sambo Dasuki ya maka Gwamnatin Shugaba Buhari a Kotu

2. Bukola Saraki

Duk da musanyawar sa, Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki na iya neman kujerar Shugaban kasar ganin yadda musamman Sanatoci ke tunzuro shi. Sai dai hakan zai yi masa wahala kwarai ganin cewa Buhari zai yi takara a 2019.

3. Adamu Garba II

Akwai wani Matashi mai suna Adamu Garba wanda ya shirya karbar mulki daga hannun Shugaba Buhari a 2019. Sai dai Saurayin yace zai tsaya takarar ne a karkashin Jam’iyyar APC wanda hakan zai yi masa wahalar cin ma burin sa yanzu.

Akwai wasu manyan ‘Yan siyasa irin su Gwamnan Jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal da sauran ‘Yan adawa irin Sule Lamido, Ibrahim Shekarau, Ahmad Makarfi, Atiku, Abubakar, Ayo Fayose da sauran su da ba mamaki su nemi kujerar Shugaban kasa a 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel