Nigerian news All categories All tags
PMB zaiyi takara a 2019 – Karanta sharhin yan Najeriya kan wannan kudiri na Buhari

PMB zaiyi takara a 2019 – Karanta sharhin yan Najeriya kan wannan kudiri na Buhari

A ranar Litinin, 9 ga watan Afrilu, hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari a shafukan zumunta, Bashir Ahmad, ya bayyana cewa shugaban kasar ya sanar da kudirinsa na sake neman zabe a 2019.

Dama dai jama’a na ta cece-kuce kan zancen ko Buhari zai sake takara a 2019, inda masana harkokin siyasa suka kayyade cewa alamunsa sun nuna cewa zai sake takara musamman da kungiyoyi da dama suka dunga rura watar ya sake takara.

Ku tuna cewa a lokacin day a halarci taron kungiyar kasashen Afrika na 5 a Abidjan, Cote d'Ivoire shugaban kasar ya bayar da Karin haske cewa zai sake neman kujera karo na biyu.

Don haka wasu yan Najeriya sun je shafukan zumunta inda suke ta tofa albarkacin bakinsu kan hukuncin shugaban kasar.

Karanta martaninsu a kasa:

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel