Nigerian news All categories All tags
Mutane 6 sun rasa rayukansu sakamakon fadan ‘yan kungiyar asiri

Mutane 6 sun rasa rayukansu sakamakon fadan ‘yan kungiyar asiri

- Mutane shida sun mutu wurin fada ‘yan kungiyar asiri wanda suka hada da birkila cikin wadanda aka kashe da bindiga sakamakon fadan

- Harbe harben ya fara ne ranar lahadi da safe wanda har ya kai kusan safiyar Litinin anayinsa

- An turajami’an tsaro da dama tun jiya zuwa unguwannin da fadan ya shafa don kawo zaman lafiya

Mutane shida sun mutu wurin fada ‘yan kungiyar asiri wanda suka hada da birkila cikin wadanda aka kashe da bindiga sakamakon fadan. Harbe-harben ya fara ne ranar lahadi da karfe 5:30 na safe a unguwar Oke- Sopen na hanyar bus stop, har ya kai zuwa Oke-Agbo da Ojowo, wanda har ya kai kusan safiyar Litinin anayinsa.

An turajami’an tsaro da dama tun jiya zuwa unguwannin da fadan ya shafa don kawo zaman lafiya, wanda suka hada da jam’ian Soji, da ‘Yan Sanda na fanni daban daban.

Jaridar the Nation ta ruwaito cewa rikicin ya farane tsakanin ‘yan kungiyar biyu dake Ijebu- Igbo, a Helikwatar dake karamar hukumar ta Ijebu da misalin karfe 5:10 na yamma, bayan an gama taron siyasa bada jimawa ba da ‘yan siyasa na gashin Ogun game da zaben 2019.

KU KARANTA KUMA: ‘Yan luwadi sunyi fada bayan kamuwa da cutar kanjamau a jihar Legas

Jami’in ‘Yan Sanda na jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, wanda ya tabbatar da arangamar, yace kwamandan unguwar na ‘Yan Sanda dake Ijebu tare da jami’an ‘Yan Sanda na Ijebuland, jami’an ‘Yan Sanda na tarayya masu kula da fashi da makami, da suran jami’an ‘Yan Sanda na jihar Ogun, duk an turasu unguwowin kuma sun tabbatar da zaman lafiya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel