Nigerian news All categories All tags
Wata mace ta gudu bayan saurayinta ya nitse a wurin wanka na Otal

Wata mace ta gudu bayan saurayinta ya nitse a wurin wanka na Otal

- Wani mutum mai suna Sikiru, mai shekaru 35, ya nitse wurin wanka na Otal, a unguwar ishashi dake jihar Legas

- Sikiru da budurwarsa sunje shan iska a Otal din mai suna Regional Hotel and Suites a ranar 2 ga watan Afirilu inda lamarin ya faru

- Budurwar ta gudu ne daga Otal din, inda manajan ya kira jami’an ‘Yan Sanda suka cire gawar daga cikin ruwan suka kaita wurin ajiyar gawa

Wani mutum mai suna Sikiru, mai shekaru 35, ya nitse wurin wanka na Otal, a unguwar ishashi dake jihar Legas.

Sikiru da budurwarsa sunje shan iska a Otal din mai suna Regional Hotel and Suites a ranar 2 ga watan Afirilu inda lamarin ya faru.

Wata mace ta gudu bayan saurayinta ya nitse a wurin wanka na Otal

Wata mace ta gudu bayan saurayinta ya nitse a wurin wanka na Otal

Budurwar ta gudu ne daga Otal din, inda manajan ya kira jami’an ‘Yan Sanda suka cire gawar daga cikin ruwan suka kaita wurin ajiyar gawa na asibitin Badagry.

KU KARANTA KUMA: ‘Yan luwadi sunyi fada bayan kamuwa da cutar kanjamau a jihar Legas

Jami’in ‘Yan Sanda mai kula da harkokin jama’a SP Chike Oti yace, binciken da jami’anmu suka gudanar akan gawar ya nuna cewa babu wani rauni a jikin gawar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel