Nigerian news All categories All tags
Babban dakin hada magunguna ya kone a Ife sakamakon tashin bam

Babban dakin hada magunguna ya kone a Ife sakamakon tashin bam

- Mutum daya ya rasa ransa sakamakon konewar babban kamfanin magunguna a Moore dake garin Ife

- Wutar ta fara ne da misalin karfe 3:30 na rana wanda yayi sanadiyar konewar magunguna na miliyoyin kudi

- Gobarar ta shafi gininnikan dake makwabtaka da kamfanin, inda jam’ian ‘Yan Sanda suka hana sintiri a unguwar

Mutum daya ya rasa ransa sakamakon konewar babban kamfanin magunguna a Moore dake garin Ife, a ranar Asabar. Wutar ta fara ne da misalign karfe 3:30 na rana wanda yayi sanadiyar konewar magunguna na miliyoyin kudi.

Gobarar ta shafi gininnikan dake makwabtaka da kamfanin, inda jam’ian ‘Yan Sanda suka hana sintiri a unguwar.

Mazauna unguwar sun fadawa manema labarai cewa an sanya bam ne a cikin kamfanin. Wani mai suna Tope ya fadawa Punch Metro cewa akwai mutum daya da ya makale a cikin ginin.

Mutumin wanda Tope ya bayyana cewa dan uwa ne ga mai kamfanin, ya samu mummunar rauni a lokacin da suka ganshi ma’aikatan kashe gobara fito dashi daga cikin ginin, kafin aka kaishi asibitin Jami’ar Awolowo, inda yam utu a ranar Lahadi.

Babban kamfanin magunguna ya kone a Ife sakamakon tashin bam

Babban kamfanin magunguna ya kone a Ife sakamakon tashin bam

Wani kuma cikin mazauna unguwar Tola, yace , “Ginin a kama wuta ne a da karfe 10 na dare a ranar Asabar. Wanda keda ginin ya rasu tun a watan Nuwamba, shekarar 2017, an samu ‘yar hatsaniya wurin rabon gado wanda ya hada da wannan ginin.

KU KARANTA KUMA: Dasuki yayi karar Malami da hukumar SSS, ya bukaci 5bn saboda sun tsareshi ba bisa ka’ida ba

Shugaban ma’aikatan kashe gobara Mista Mike Ogundipe ya fadawa Punch Metro cewa mutanensa sun kashe wutar, sun koma ranar Lahadi, don tabbatarwa da wutar bata sake tashi ba.

Jami’ar ‘Yan Sanda mai kula da harkokin jama’a ta jihar Osun, Misis Folasade Odoro, lokacin da aka nemeta a wayar salula tace zata yanda lamarin yake ta sake kira, amma dai har yanzu bata kira ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel