Nigerian news All categories All tags
Dasuki yayi karar Malami da hukumar SSS, ya bukaci 5bn saboda sun tsareshi ba bisa ka’ida ba

Dasuki yayi karar Malami da hukumar SSS, ya bukaci 5bn saboda sun tsareshi ba bisa ka’ida ba

- Tsohon mai bawa shugaban kasa shawara ta fannin tsaro Sambo Dasuki, ya sake shigar da kara akan hukumar ‘Yan Sanda masu farin kaya

- Dasuki ya bukaci hukumar da ta sakeshi ba tare da wani dalili ba

- Dasuki, tsohon kanal ne wanda aka tsare tin a ranar 29 ga watan Disamba, 2015, ya bukaci hukumar ta bashi 5bn na daurin da tayi masa

Tsohon mai bawa shugaban kasa shawara ta fannin tsaro Sambo Dasuki, ya sake shigar da kara a kotun tarayya dake birnin tarayya game da rukon da hukumar ‘Yan Sanda masu farin kaya sukeyi masa.

Dasuki ya bukaci hukumar da ta sakeshi ba tare da wani dalili ba. Dasuki, tsohon kanal ne wanda aka tsare tin a ranar 29 ga watan Disamba, 2015, ya bukaci hukumar ta bashi 5bn na daurin da tayi masa da kuma shiga hakkinsa.

A karar da ya shigar mai lambaFHC/ABJ/CS/263/2018 wadda aka shigar a ranar 15 ga watan Maris 2018, ya bukaci kotun da ta sanya mutane uku wadanda zasu tabbatar da an buga a manyan jaridu guda biyu na cewa sun bashi hakuri na keta hakkinsa da hukumar tayi kamar yadda yake a sashe na 35(1), (4), da (5), 37 da 41(1) na dokar kasa ta 1999.

Darakta Janar na hukumar DSS, Lawal Daura, da hukumar da Kanta, da kuma Atony Janar na tarayya, Abubakar Malami, an shigar dasu a matsayin wadanda ake kara, wadda Justice Ahmed Mohammed ke shari’ar a kotun tarayya duk da ba’a kaiga sa ranar sauraren karar ba.

KU KARANTA KUMA: Iska ne ya jeho hodar iblis cikin jakar hannuna – Wata mata ga yan sanda

Hukuncin da kotun kungiyar tattalin arzikin jihohin Afirika ta Yamma ta yanke wanda ta yanke a ranar 4 ga watan Oktoba, 2016, ta bayar da izinin a saki tsohon NSA daga hannun hukumar DSS wanda har yanzu tarayyar Najeriya bata bi waddan umurni ba. Kotun tace rukon nasa ya sabawa doka ta bayar da umurnin gwamnatin tarayya da ta bashi N15m na hakkin tsaron da tayi masa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel