Nigerian news All categories All tags
Rundunar sojin saman Najeriya sun samu nasarar dakile wani harin bam da 'yan kungiyar Boko Haram suka yi shirin kaiwa jami'ar Maiduguri

Rundunar sojin saman Najeriya sun samu nasarar dakile wani harin bam da 'yan kungiyar Boko Haram suka yi shirin kaiwa jami'ar Maiduguri

- Rundunar sojin saman Najeriya (NAF) tare da hadin gwiwar rundunar sojin kasan Najeriya (NA), sun dakile wani yunkuri harin bam da 'yan ta'addar kungiyar Boko Haram suka yi kokarin kai wa cikin jami'ar Maiduguri dake jihar Borno, a ranar 8 ga watan Afirilun nan da daddare.

Rundunar sojin saman Najeriya sun samu nasarar dakile wani harin bam da 'yan kungiyar Boko Haram suka yi shirin kaiwa jami'ar Maiduguri

Rundunar sojin saman Najeriya sun samu nasarar dakile wani harin bam da 'yan kungiyar Boko Haram suka yi shirin kaiwa jami'ar Maiduguri

Rundunar sojin saman Najeriya (NAF) tare da hadin gwiwar rundunar sojin kasan Najeriya (NA), sun dakile wani yunkuri harin bam da 'yan ta'addar kungiyar Boko Haram suka yi kokarin kai wa cikin jami'ar Maiduguri dake jihar Borno, a ranar 8 ga watan Afirilun nan da daddare.

DUBA WANNAN: Sarkin Musulmi ya gargadi matasa akan bangar siyasa a zaben 2019

'Yan kungiyar ta Boko Haram sunyi kokarin shiga jami'ar ta Maiduguri Allah bai basu sa'a ba, inda a take sojojin suka gane manufar su, suka yi kokarin dakatar da harin, yayinda wani daga cikin masu kai harin bam din ya tashi dashi tun kafin ya samu damar shiga makarantar.

Har yanzu dai babu wani labari dake nuna cewar wani ya rasa ranshi banda dan Boko Haram din da ya mutu, wanda abokanan sa suka gudu bayan sun gane cewar an gano manufar su, sai dai hakar su bata cimma ruwa ba, domin kuwa sojojin sun bude musu wuta, yayinda wasu daga cikin su suka nausa daji sojojin sama suka bisu da jirage suka kashe da yawa daga cikin su. Har yanzu dai rundunar sojin saman tana nan tana ta faman binciken ind sauran suka boye.

An kuma shawarci al'ummar yankin musamman ma daliban da suke makarantar dasu dinga lura da irin mutanen da suke shige da fice a yankin makarantar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel