Nigerian news All categories All tags
Iska ne ya jeho hodar iblis cikin jakar hannuna – Wata mata ga yan sanda

Iska ne ya jeho hodar iblis cikin jakar hannuna – Wata mata ga yan sanda

Wata mata yar kasar Amurka ta zargi iska mai karfi da sanya mata hodar iblis da aka kama ta da shi

Yan sanda sun kasa Kennecia Posey bayan wani tsayawa a Fort Pierce, Florida, a ranar 21 ga watan Maris, a cewar rahotanni daga ABC local affiliate.

Rahoton ya kawo cewa yan sanda da aka tsame daga lamarin sun bayyana cewa wani jami’i ya tunkari motar Ms Posey sannan ya ji warin ganye wanda ke fita daga cikin motan.

Amma lokacin da jami’in ya cigaba da bincike ya gano wani jaka dake kunshe da hodar iblis da ganye a kan cinyanta.

Iska ne ya jeho hodar iblis cikin jakar hannuna – Wata mata ga yan sanda

Iska ne ya jeho hodar iblis cikin jakar hannuna – Wata mata ga yan sanda

Ms posey mai shekaru 26 ta amince da cewar itace mammalakiyar ganyen, amma ta bayar da wani uziri mai ban al’ajabi akan hodar iblis din.

KU KARANTA KUMA: Masu mota sun yabama Dangote kan aikin titin Obajana-Kabba

“Bani da masaniya akan ko wani hodar iblis,” inji ta, a cewar rahoton. “Rana ce mai cike da guguwa. Babu mamaki iska ne ya jeho shi ya taga sannan ya shige jakata."

An tura Ms Posey gidan kurkuku sakamakon kamata da akayi da hodar Iblis da kuma ganye. Daga baya an sake ta bayan yarjejeniya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel