Nigerian news All categories All tags
Sarkin Musulmi ya gargadi matasa akan bangar siyasa a zaben 2019

Sarkin Musulmi ya gargadi matasa akan bangar siyasa a zaben 2019

- Mai girma sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar, yayi gargadi ga matasa gabannin zaben shekarar 2019, inda shi kuma mai martaba sarkin Kano Sunusi Lamido Sunusi, ya jinjinawa shugabannin siyasar kasar nan wajen kokarin da suke na ganin sun martaba masarautun gargajiya

Sarkin Musulmi ya gargadi matasa akan bangar siyasa a zaben 2019

Sarkin Musulmi ya gargadi matasa akan bangar siyasa a zaben 2019

Mai girma sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar, yayi gargadi ga matasa gabannin zaben shekarar 2019, inda shi kuma mai martaba sarkin Kano Sunusi Lamido Sunusi, ya jinjinawa shugabannin siyasar kasar nan wajen kokarin da suke na ganin sun martaba masarautun gargajiya.

DUBA WANNAN: Muna da hanyoyin da zamu bi don ganin mun gyara Najeriya - Abduljalil Tafawa Balewa

Sarakan sun hadu ne a wajen taron bikin taya sarkin Ningi na 16, Mai Martaba Alhaji Yunusa Danyaya, murnar cika shekaru 40 akan karagar mulkin masarautar ta Ningi.

Mai girma sarkin Musulmin ya baiwa al'umma shawara musamman ma matasa cewar ganin yanda lokacin zabe yake kara karatowa, kada wanda ya sake 'yan siyasa suka yi amfani dashi da kudi ko wani abu makamancin haka wurin jefa shi cikin harkar bangar siyasa.

Har ila yau mai alfarman yayi kira ga kowa da kowa yaje yayi rijistar zabe domin yin amfani da ita wurin zaben shugabannin da suka dace, da kuma kawar da baragurbin shugabanni a kasar nan.

A lokacin da yake jawabin shi, Mai Martaba sarkin Kano, ya jinjinawa manya-manyan shugabannin siyasa akan kokarin da suke wurin ganin sun martaba masarautun gargajiya, don daraja tarihi da kuma kawo hadin kai don a taimakawa al'umma.

A hirar da yayi da manema labarai, Mai Martaba sarkin Ningi Alhaji Muhammadu Yunusa Danyaya, yayi bayani ne akan matsayar masarautun gargajiya a kundin tsarin mulkin kasar nan.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel