Nigerian news All categories All tags
Yadda gwamnatin Najeriya ta bari Boko Haram suka zamo masu arziki - Kukah

Yadda gwamnatin Najeriya ta bari Boko Haram suka zamo masu arziki - Kukah

Babban fasto din cocin Roman Catholic Diocese dake Sokoto, Mathew Kukah, yayi zargin cewa gwamnatin Najeriya ta sa yan ta’addan Boko Haram sun zamo masu kudi ta hanyar kudin fansa.

Mista Kukah yace akwai bukatar gwamnati tayi gaggawan sauraron korafe-korafen mutane sannan ta sanya fuskar tausayi wajen kawo karshen ayyukan ta’addanci a arewa maso gabas.

Babban limamin cocin, a lokacin wani hira da gidan talbijin din Channels, ‘Hard Copy’ a ranar Lahadi, ya bayyana cewa gwamnatin ta rage yaki da take da ta’addanci zuwa ga ayyukan sojoji kawai sannan ta gaza magance tushen matsalar.

Yadda gwamnatin Najeriya ta bari Boko Haram suka zamo masu arziki - Kukah

Yadda gwamnatin Najeriya ta bari Boko Haram suka zamo masu arziki - Kukah

KU KARANTA KUMA: Masu mota sun yabama Dangote kan aikin titin Obajana-Kabba

Yace sace yan matan makarantar Dapchi ya rusa ikirarin cewa an gurgunta Boko Haram da kuma tattaunawa da yan ta’addan domin neman mafita.

A baya Legit.ng ta kawo cewa Mutum guda daya ya gamu da ajlinsa, inda ya rigamu gidan gaskiya a wani tashin bom da aka samu a ranar Asabar 7 ga watan Afrilu a jihar Osun, wanda ya ragargaza wani katafaren gidan sama, inji rahoton gidan talabijin na Channels.

Wannan mummunan lamari ya faru ne a layin Moore, dake garin Ile Ife na jihar Osun, inda zamauna ungwuar suka tabbatar da cewar wani karamin Bom aka dana a gidan, sai dai Yansanda basu tabbatar da hakan ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel