Nigerian news All categories All tags
Dolene a sanar da jama'a masu sace musu dukiyar kasa - Adam Oshiomhole

Dolene a sanar da jama'a masu sace musu dukiyar kasa - Adam Oshiomhole

-

Dolene jama'a su san masu sace musu dukiyar kasa - Adam Oshiomhole

Dolene jama'a su san masu sace musu dukiyar kasa - Adam Oshiomhole

Tsohon gwamnan jihar Edo, Comrade Adams Oshiomhole yace gwamnatin tarayya tayi daidai da ta bayyana wadanda suka wawure kudade saboda yan'najeriya suna da hakkin sanin wadanda suka sace musu kudi.

DUBA WANNAN: A yau ne za a gudanar da taron jam'iyyar APC a Abuja domin neman mafita ga masu neman karin wa'adi

A ranar 30 ga watan Maris zuwa 1 ga watan Afirilu ne gwanatin tarayya ta saki sunayen mutanen da suka sace kudin kasar nan, abin da ya ba wa mutane da dama mamaki kuwa shine, yawancinsu yan jam'iyyar adawa ta PDP ne.

Oshiomhole yayi kira ga hukumar yaki da cin hancin da rashawa (EFCC) da su yi aikin da ya dace akan dukkan mutanen da sunansu ya bayyana domin karin karfin guiwa ga yaki da rashawa da Shugaba muhammadu Buhari yasa gaba.

A karshen makon nan ne Oshiomhole yayi magana da manema labarai bayan walimar bikin yar' Dan majalisar dokoki mai wakiltar Ikpoba-Okha/Egor ta jihar Edo, Hon. Ehiozuwa Agbonayinma.

"Bukata ta itace yakamata gwanatin tarayya ta daina tausayawa mahandama saboda akwai mutane da dama da ya kamata suna kotu amma har yanzu shiru kake ji suna nan suna cigaba da rayuwa cikin walwala kamar kowa. Sun saci makuden kudade, bazamu dinga jaje ba a yau bayan munsan wadanda suka wawure kudaden, a tsarin damokaradiyya shine mutane na da hakkin sanin abinda ke faruwa, ko mai kyau, ko akasin hakan.

Tsohon shugaban kungiyar kwadago ta kasa (NLC) ya shawarci yan kasa dasu yi taka tsantsan gurin mu'amala da mutanen da ke da muguwar manufa masu neman mulki don bukatar kansu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel