Nigerian news All categories All tags
Muna da hanyoyin da zamu bi don ganin mun gyara Najeriya - Abduljalil Tafawa Balewa

Muna da hanyoyin da zamu bi don ganin mun gyara Najeriya - Abduljalil Tafawa Balewa

-

Muna da hanyoyin da zamu bi wurin ganin mun kada jam'iyyar APC daga kan mulki - Abduljalil Tafawa Balewa

Muna da hanyoyin da zamu bi wurin ganin mun kada jam'iyyar APC daga kan mulki - Abduljalil Tafawa Balewa

Gabatowar zaben 2019, shuwagabannin kungiyar taimakon gaggawa ta Najeriya ( Nigeria Intervention Movement) wanda ake kira "Third Force" a jiya ne suka ce sun shirya tsaf don fitar da kasar halin da take ciki.

DUBA WANNAN: Buhari na cigaba da samun goyon bayan jam'iyya

A taron da jiga jigan kungiyar sukayi a Legas, shugaban kungiyar na kasa, Dr. Olisa Agbakoba (SAN) yace duk da su ba jam'iyyar siyasa mai rijista bane, amma kungiyar ta kammala shirye shiryen yanda zasu fitar da shuwagabannin yanzu su maye gurbinsu da sababi ta hanyar amfani da karfin kuri'u.

Mai magana da yawun kungiyar, Agbakoba yace "wannan ne taron mu na farko bayan wanda mukayi a Abuja. Muna tattauna hanyoyin cigaba. Mun gano cewa miliyoyin yan Najeriya na tare da yunwa, talauci, rashin aikin yi sannan basu da damar samun karatu mai inganci, kiwon lafiya da sauransu.

" Tunda muka ga zabe na matsowa, burin mu na farko shi ne mu tsara yanda abin zai kasance a fadin kasar kuma mu tabbatar da mun ceto kasar daga hannun shuwagabannin yanzu. Muna burin ganin yan Najeriya sun rike kasarsu domin amfaninsu.

Mataimakin shugaban kungiyar Abduljahlil Tafawa Balewa yace" tunda kungiyar ba ta siyasa bace, mataki na farko shine tsarawa da wayar da kan yan kasar.

Abduljahlil yace kwalliya tana biyan kudin sabulu kuma lokaci kawai ake jira domin aga amfanin wayar da kai.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel