Nigerian news All categories All tags
Jerin barayi: Sunayen da aka saki a baya sobin-tabi ne Inji Gwamnatin Buhari

Jerin barayi: Sunayen da aka saki a baya sobin-tabi ne Inji Gwamnatin Buhari

- Gwamnatin Buhari za ta fito da sunayen barayin da zai girgiza jama’a

- Ministan labarai Lai Mohammed yace jama’a ba su ga komai ba tukun

- Lai yace babu wanda ya isa ya hana a bayyana sunayen barayin kasar

Ministan yada labarai da al’adu a Gwamnatin Buhari watau Lai Mohammed ya bayyana cewa sunayen barayin kasar nan da za a fitar ba da dadewa ba zai ba kowa mamaki a Najeriya. Lai yace sunayen da aka fitar a baya ba komai bane.

Jerin barayi: Sunayen da aka saki a baya sobin-tabi ne Inji Gwamnatin Buhari

Lai Mohammed yace Gwamnatin Buhari za tabayyana wasu barayin kasar. (Daga Daily Trust)

Kwanakin baya an saki sunaye na wadanda ake zargi da satar dukiyar al’umma. Ministan labaran kasar Mohammed yace kwanan nan ne kuma ake sa rai cewa Gwamnatin Shugaba Buhari za ta saki sunayen wasu barayin da ba a bayyana ba a baya.

KU KARANTA: Za a saki sunayen wasu Barayin Najeriya kwanan nan

Lai Mohammed ya maida martani ga masu shirin shiga Kotu bayan an sa sunan su a cikin barayin kasar inda yace sai sun dawo don kuwa yana da hujjojin sa. Lai Mohammed yace babu kuma wanda ya isa ya hana a fitar da jerin ragowar barayin kasar.

Ministan yayi wannan bayani ne lokacin da ya kai ziyarar ta’aziya wajen Gwamnan Jihar Kwara Abdulfatah Ahmed na barnar da aka yi a Garin Offa a makon da ya gabata. Lai yace har wadanda ba a tunani sun yi mugun barna a Najeriya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel