Nigerian news All categories All tags
An gano shugaban Najeriya da ya fi ragowar kwarewa a cin hanci, an fadi adadin kudinsa kafin hawa mulki

An gano shugaban Najeriya da ya fi ragowar kwarewa a cin hanci, an fadi adadin kudinsa kafin hawa mulki

A jiya ne tsohon gwamnan jihar Abiya, Orji Uzor Kalu, ya yi watsi da kashedin da gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya yi masa na cewar, kul ya kuskura ya shiga jihar Ekiti domin yiwa Buhari yakin neman zabe.

Tsohon gwamna Kalu ya caccaki tsohon shugaban kasa Obasanjo tare da bayyana shi a matsayin shugaban Najeriya da ya kware a cin hanci da rashawa.

Kazalika, ya bayyana cewar, Obasanjo, bashi da kimar da zai rubuta wasika yana shawartar Buhari ya hakura da tsayawa takara a 2019.

An gano shugaban Najeriya da ya fi ragowar kwarewa a cin hanci, an fadi adadin kudinsa kafin hawa mulki

Orji Kalu da Obasanjo

Da yake magana a kan irin yadda Obasanjo ya barnatar da dukiyar Najeriya, Kalu, ya ce, "idan ku ka duba bayanan ku da kyau, zaku yarda da ni cewar, Najeriya bata taba yin shugaba da ya fi Obasanjo iya tafka sata ba. Lokacin da ya aka tsayar da shi takarar shugaban kasa bashi da kudin da ya kai N20,000 amma kafin ya bar mulki ya mallaki gonar biliyoyin Naira a Otta bayan katafaren gida da dakin karatu da ya gina."

DUBA WANNAN: Hukumar kwastam tayi babban kamu a jihohin Kano da Jigawa, ta cafke mutane hudu

Kalu ya kara da cewar, "koda wani zai bawa Buhari shawara, to tabbas babu Obasanjo cikin irin wadannan mutanen."

Kalu ya bukaci 'yan Najeriya da su manta da duk wani batun rubuta wasikar bawa Buhari shawarar sake tsayawa takara tare da bayyana cewar, Buhari ya cancanci tazarce saboda ya daga tattalin arzikin Najeriya daga Dala biliyan $23bn zuwa biliyan $47bn.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel