Nigerian news All categories All tags
Nadin da Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki yayi ya jawo ce-ce-ku-ce

Nadin da Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki yayi ya jawo ce-ce-ku-ce

Mun kawo yadda Abubakar Danladi ya taba zama Mataimakin Gwamnan Taraba bayan nan kuma aka tsige shi. Daga baya kuma ya dawo Gwamna har ya zama Sanata a karshe ya tashi a tutar-babu duk a cikin ‘dan lokaci kan-ka-ni.

Mun fahimci cewa nadin da Shugaban Majalisar Dattawa watau Bukola Saraki yayi na tsohon Gwamnan Taraba mai shekaru 53 a Duniya kuma Sanata a-da watau Abubakar Danladi ya jawo ce-ce-ku-ce a kasar saboda wasu dalilai.

Nadin da Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki yayi ya jawo ce-ce-ku-ce

Tsohon Sanata ya zama Hadimin Bukola Saraki a Majalisa

Wani Matashi kuma Mutumin Jihar Taraba mai suna Abubakar Usman Leme ya bayyana cewa a lokacin Marigayi Danbaba Suntai yana Gwamna aka tsige Danladi daga Mataimakin Gwamna wanda daga baya kuma aka yi kutun-kutun na maido sa.

KU KARANTA: Rigimar mu da Buhari ba za ta kare ba - Bukola Saraki

An dawo da shi kujerar Mukaddashin Gwamna ne domin a tsige wanda ya hau kujerar Gwamna Suntai a lokacin. Bayan Danladi ya zama Gwamna ne ake zargin an yi amfani da shi wajen murde zaben da Arch. Darius Ishaku yayi nasara a 2015.

Wasu na zargin cewa an yi wa Abubakar Danladi alkawarin kujerar Sanata ne bayan nan wanda kuma daga karshe Kotu ta tsige shi. Daga sauya sheka zuwa Jam’iyyar APC ne kuma sai ga shi Bukola Saraki ya nada shi Hadimin sa a kwanan nan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel