Nigerian news All categories All tags
Gwamnan Ribas ya bayyana yadda Gwamnatin Tarayya ke nufin sa da sharri

Gwamnan Ribas ya bayyana yadda Gwamnatin Tarayya ke nufin sa da sharri

- Gwamnan Jihar Ribas yace Gwamnatin Tarayya na neman ganin bayan sa

- Nyesom Wike yace ana kokarin hada masa wani sharri domin ayi ram da shi

- Gwamnan dai yace ana neman yi masa irin abin da aka yi wa Alamieseigha

Labari ya zo mana cewa Gwamnan Jihar Ribas watau Nyesom Wike ya koka da cewa Gwamnatin Tarayya na neman sa da sharri domin a ga bayan sa kamar yadda aka yi wani tsohon Gwamna. Saidai yace ko kadan abin bai ba shi tsoro.

Gwamnan Ribas ya bayyana yadda Gwamnatin Tarayya ke nufin sa da sharri

Gwamnan Ribas Nyesom Wike ya koka da Gwamnatin Buhari

Gwamna Nyesom Wike ta bakin wani Hadimin sa Simeon Nwakaudu ya bayyana mana cewa Gwamnatin Tarayya na shirin jefa sa cikin bala’i ta hanyar amfani da Jami’an tsaro a damke sa a kasar waje da zarar ya bar kasar nan.

KU KARANTA:

Nyesom Wike yace za ayi kokarin a rutsa shi a masaukin sa idan ya bar Najeriya sai ayi masa sharrin cewa an samu makudan kudi a hannun sa wanda hakan ya sabawa dokar kasa. Wike yace wannan zalunci ne kuma abin takaici.

Gwamnnan yace abin da aka yi wa Marigayi tsohon Gwamnan Bayelsa Cif DSP Alamieseigha ake nema ayi masa amma yace ba za su kai labari ba. Gwamnan yace ana kokarin hana ‘Yan adawar Gwamnatin nan sakat ne amma an makara.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel