Wani Bom ya tashi a jihar Osun, yayi raga raga da wani gidan sama
Mutum guda daya ya gamu da ajlinsa, inda ya rigamu gidan gaskiya a wani tashin bom da aka samu a ranar Asabar 7 ga watan Afrilu a jihar Osun, wanda ya ragargaza wani katafaren gidan sama, inji rahoton gidan talabijin na Channels.
Wannan mummunan lamari ya faru ne a layin Moore, dake garin Ile Ife na jihar Osun, inda zamauna ungwuar suka tabbatar da cewar wani karamin Bom aka dana a gidan, sai dai Yansanda basu tabbatar da hakan ba.
KU KARANTA: Yaki da yan bindiga: Yansanda sun kwato manyan bindigu guda 84 a jihar Kaduna
Wani rahoto da Legit.ng ta kalato ya bayyana cewar an shiga zaman dardar tun bayan lamarin, wanda ya sanya makwabtan gidan tserewa don tsiratar da rayukansu, musamman duba da tashin bom din ya faru ne da misalin karfe 11 na dare, a lokacin da kowa ke kwance.
Majiyar ta kara da cewa a sakamakon tashin bom din, wani mutum guda ya samu munanan rauni, wanda hakan yayi sanadin mutuwarsa bayan an garzaya da shi Asibiti.
Sarkin Ife, Oba Enitan Adeyeye Ogunwusi ya bayyana cewar tun a baya akwai rikita rikitan gado a tsakanin yan uwan asalin Maigidan, amma ya bada tabbacin zasu shiga maganan don kawo sulhu a tsakani.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng