Nigerian news All categories All tags
Buhari na cigaba da samun goyon bayan jam'iyya

Buhari na cigaba da samun goyon bayan jam'iyya

- Kwamitin jam'iyyar APC mai mulki sun bawa shugaban kasa Muhammadu Buhari goyon baya dari bisa dari, akan zaben da za a gudanar na shugabannin jam'iyya, domin farawa daga kan matakin karamar hukuma har zuwa matakin shugabannin jam'iyyar na kasa

Buhari na cigaba da samun goyon bayan jam'iyya

Buhari na cigaba da samun goyon bayan jam'iyya

Kwamitin jam'iyyar APC mai mulki sun bawa shugaban kasa Muhammadu Buhari goyon baya dari bisa dari, akan zaben da za a gudanar na shugabannin jam'iyya, domin farawa daga kan matakin karamar hukuma har zuwa matakin shugabannin jam'iyyar na kasa.

DUBA WANNAN: A yau ne za a gudanar da taron jam'iyyar APC a Abuja domin neman mafita ga masu neman karin wa'adi

A zantawar da yayi da manema labarai jiya a Abuja kakakin kwamitin jam'iyyar, Jock Alamba, wanda Nasir Danu da Omolaoye Akintola, sakataren jam'iyyar suka sanya hannu, sun bayyana kudurin shugaban kasa Muhammadu Buhari akan bin dokar da jam'iyya ta gindaya, domin tabbatar tsarin mulki na demokradiyya.

A taron da aka gabatar da na karshe, shine kwamitin jam'iyyar ta janye kudurin ta na goyawa shugaban jam'iyyar Cif John Odigie Oyegun da kuma wasu manya daga cikin shugabannin jam'iyyar baya akan karin wa'adin da suka nema na tsawon shekara daya.

A ranar 21 ga watan Maris na wannan shekarar, kwamitin ta yi kira ga shugabannin jam'iyyar da su dauki hukunci mai karfi akan wasu daga cikin mambobin kungiyar da suka kai karar jam'iyyar zuwa kotu akan karin wa'adin da wasu suke so na shekara daya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel