Nigerian news All categories All tags
A yau ne za a gudanar da taron jam'iyyar APC a Abuja domin neman mafita ga masu neman karin wa'adi

A yau ne za a gudanar da taron jam'iyyar APC a Abuja domin neman mafita ga masu neman karin wa'adi

- Majiyar mu Legit.ng ta tabbatar da cewar shugaban kasa Muhammadu Buhari zai halarci taron a yau kafin ya tafi kasar Ingila

- Akwai yiwuwar za'a dauki mataki na karshe a yau game da matsalar karin wa'adi da jam'iyyar ta ke fuskanta

A yau ne za a gudanar da taron jam'iyyar APC a Abuja domin neman mafita ga masu neman karin wa'adi

A yau ne za a gudanar da taron jam'iyyar APC a Abuja domin neman mafita ga masu neman karin wa'adi

A yau ne kwamitin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) zata gudanar da taron ta na kasa a birnin tarayya Abuja.

Majiyar mu Legit.ng ta tabbatar da cewar shugaban kasa Muhammadu Buhari zai halarci taron a yau kafin ya tafi kasar Ingila. Mataimakin Daraktan jam'iyyar ta APC, Edegbe Odemwingie, shine ya tabbatar da hakan ga manema labarai jiya a Abuja.

DUBA WANNAN: Alamomi guda 20 na Cutar Cancer da ya kamata kowa ya sani

Sakataren jam'iyyar, Malam Bolaji Abdullahi, ya shaidawa manema labarai a ranar juma'an nan data gabata cewar jam'iyyar ta fara gabatar da shriye-shiryen taron ne kafin ta sanarwa da jama'a ranar Larabar da ta gabata.

Bayanin da yayi ya tabbatar da cewar taron da jam'iyyar ta ke so ta yi na gaggawa zai bawa 'yan kwamitin damar zuwa taron har na tsawon kwanaki bakwai.

Akwai yiwuwar za'a dauki mataki na karshe a yau game da matsalar karin wa'adi da jam'iyyar ta ke fuskanta, bayan rahoton da kwamitin ta bayar juma'ar data gabata wanda aka kafa ta karkashin 'yan kwamiti 10, inda gwamnan jihar Filato Simon Lalong ya jagoranta.

Kwamitin ya bada shawarar a gabatar da sabon taron jam'iyya bayan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu goyon bayan daga gwamnonin jam'iyyar. A taron da aka gudanar a watan Fabrairun wannan shekarar hukumar ta NEC ta amince da a kara wa'adin shekara daya ga shugaban jam'iyyar, Cif John Odigie Oyegun da kuma wasu daga cikin manya-manyan shugabannin jam'iyyar.

Sai dai kuma a ranar 27 ga watan Mayu, a taron da hukumar ta NEC ta gabatar, shugaban kasa Muhammadu Buhari yace sakamakon da aka gabatar na kara wa'adin shekara daya ga shugabannin jam'iyyar ya sabawa tsarin jam'iyyar APC dama tsarin dokar kasa gaba daya.

A yau ne ake sa ran za'a sake gudanar da sabon taron domin a tsayar da mafita ga bukatun mambobin jam'iyyar. Tuni aka gabatar da Gwamnan jihar Jigawa Alhaji Abubakar Badaru a matsayin shugaban kwamitin tsare-tsare na taron da za a gudanar.

A taron da aka gabatar a baya, mai magana da yawun jam'iyyar ta APC yace jam'iyyar ta amince da cewa za'a kafa kwamiti tsakanin majalisar dattawa, da majalisar zartaswa, domin duba muhimman abubuwan da aka tattauna akai, domin bawa shugaban kasa mika tsare-tsaren ga majalisar dokoki domin gabatar da aiki akai.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel