Nigerian news All categories All tags
Sojoji sun yi batakashi da makiyaya a jihar Taraba, sun kashe 1, sun kama 3

Sojoji sun yi batakashi da makiyaya a jihar Taraba, sun kashe 1, sun kama 3

Runduna ta musamman, na 72 a Sojin kasa ta batakashi da makiyaya yan bindiga a jihar Taraba, a yayin aikin kakkabe yan bindiga daga kauyukan Gbajimba, Baka, Tomanyi, Iyode da Dogon Yashi.

Kaakakin rundunar Soja, Birgediya Texas Chukwu ya sanar da haka a ranar Lahadi 8 ga watan Afrilu, inda yace Sojoji sun yi arangama da yan bindiga makiyaya da misalin karfe 1330, kuma sun kashe guda daga cikinsu, tare da jikkata guda, haka zalika suma kama guda uku.

KU KARANTA: Wasu miyagun mutane sun rataye wata budurwa a gidan iyayenta dake jihar Kano

Gidan talabijin na Channels ta ruwaito Kaakakin ya cigaba da fadin bayan Sojoji sun fi karfinsu, sun kwato bindiga kirar AK 47. Hakazalika Sojoji dake sintiri a yankin jatoaka na jiha Taraba sun kama gungun yan fashi na mutum 10, inda tuni sun mika su ga jami’an Yansanda don gudanar da bincike.

Sojoji sun yi batakashi da makiyaya a jihar Taraba, sun kashe 1, sun kama 3

Sojoji

A wani labarin kuma, Texas Chukwu ya bayyana cewar wani babban kwamandan Boko Haram ya mika wuya ga Sojoji a dajin Sambisa, wanda a yanzu haka yana amsa tambayoyi a Birget ta 26.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel