Nigerian news All categories All tags
Wani Kwamandan Boko Haram ya karkashe jama’a bayan Gwamnati ta sake shi saboda yan matan Chibok

Wani Kwamandan Boko Haram ya karkashe jama’a bayan Gwamnati ta sake shi saboda yan matan Chibok

A shekarar da ta gabata ne dai gwamnatin tarayya ta saki wasu manyan kwamandojin Boko Haram da nufin kungiyar ta sako yan matan Chibok da take tsare dasu tun a shekarar 2014, sai sahihan rahotanni sun tabbatar guda daga cikin kwamandojin, Shuaibu Moni ne ya kai wani mummunan hari a ranar bikin Ista.

Daily Nigerian ta ruwaito a ranar 1 ga watan Afrilu ne al’ummar yankin Bale Kura, Bale Shuwarin, Jmaine da Alikaramti duk a cikin karamar hukumar Jere, suka fuskanci munanan hare har da suka yi sanadin mutuwar mutane 29, tare da jikkata 83, harin da Moni ya shirya kuma ya jagoranta.

KU KARANTA: Wasu miyagun mutane sun rataye wata budurwa a gidan iyayenta dake jihar Kano

Dama dai majiyar Legit.ng ta ruwaito kimanin kwanaki uku kacal da sako yan matan na Chibok ne Moni yayi bidiyo, inda a ciki yake aika sakon cewar zai cigaba da kunar bakin wake tare da kai hare hare a Najeriya.

Wani Kwamandan Boko Haram ya karkashe jama’a bayan Gwamnati ta sake shi saboda yan matan Chibok

Shuaibu

Bugu da kari, a kokarin gwamnati na ceto yan matan Dapchi da kungiyar Boko Haram bangaren Abu Mus’ab Al-Barnawi, Gwamnati ta sakar musu wani babban kwamandansu, Hussaini Maitangaran, wanda shi ne ya jagoranci hare haren da aka kai jihar Kano a ranar 20 ga watan Janairun 2012, da kuma harin da aka kai a Masallacin Sarki na jihar Kano, inda aka yi asarar daruruwan rayuka.

Babbar fargabar da ake fama da ita a Arewa maso gabas a yanzu shi ne, Moni ya kafa wata sabuwar rundunar yan ta’adda da zata dinga kai hare haren kunar bakin wake, da kuma satar mutane, inda daga sako yan matan Chibok zuwa yanzu, Moni ya kai hare haren kunar bakin wake guda 15, tare da kai ma yan gudun hijira hari

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel