Nigerian news All categories All tags
Sama da kasa ba za su hade ba idan aka kama Obasanjo, Jonathan da su IBB – Farfesa

Sama da kasa ba za su hade ba idan aka kama Obasanjo, Jonathan da su IBB – Farfesa

- Wasu na ganin zai yi wahala a kama irin su Jonathan da Janar Obasanjo a Najeriya

- Shi kuwa wani babban Farfesa yace sama da kasa ba za su hade don an damke su ba

- Farfesan yace kasar za ta zama kamar ba ayi ba idan aka nemi a binciki shugabannin

Mun samu labari cewa wani rikakken Farfesan harshe ‘Dan Najeriya da ke kasar waje watau Pius Adesanmi ya nemi Allah ya kawo ranar da za a kama tsofaffin Shugaban kasar nan a bincike su.

Sama da kasa ba za su hade ba idan aka kama Obasanjo, Jonathan da su IBB – Farfesa

Wani Farfesa ya nemi a kama tsofaffin Shugaban kasar nan

Farfesa Pius Adesanmi yace ba abin da zai faru duk ranar da aka samu wani Gwamnati mai hankali da ta shirya binciken Shugabannin da su ka mulki Najeriya a baya irin su Goodluck Jonathan, da kuma Olusegun Obasanjo.

KU KARANTA: Wani fitaccen Sanata ya kuma yin Allah-wadai da kashe-kashen da aka yi a Offa

Babban Malamin Jami’ar ya bayyana cewa sai an ma fi da zaman lafiya idan aka kama tsofaffin Shugabannin kasar nan irin su JanarIbrahim Babangida da Abdussalami Abubakar aka bincike irin barnar da su ka tafka.

Wasu dai na ganin cewa tsofaffin Shugabannin na Najeriya sun fi karfin bincike sai dai wannan babban malami yace kowa zai cigaba da sabgogin gaban sa ne kamar yadda aka saba idan su Obasanjo su ka shiga hannun Hukuma.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel