Nigerian news All categories All tags
Offa: Dole Gwamnati ta kare rayuka da dukiyoyin Jama’a - Kwanwkaso

Offa: Dole Gwamnati ta kare rayuka da dukiyoyin Jama’a - Kwanwkaso

- Kwankwaso ya nemi Gwamnatin Tarayya ta kara kokarin wajen harkar tsaro

- ‘Dan Majalisar yayi tir da abin da ya faru a Garin Offa a makon jiya da ya wuce

- Shi ma Saraki yace akwai bukatar Hukuma ta inganta harkar tsaro a kasar nan

Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma Sanata a Majalisar Dattawa Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso yayi tir da fashin da aka yi kwanan nan a Garin Offa da ke cikin Jihar Kwara inda ya nemi a dauki mataki.

Offa: Dole Gwamnati ta kare rayuka da dukiyoyin Jama’a - Kwanwkaso

Injiniya Kwanwkaso ya nemi Gwamnati ta dage a bangaren tsaro

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso yayi amfani da shafin sa na Tuwita yayi Allah-wadai da mummunan abin da ya faru a Jihar Kwara inda mutane akalla 30 su ka mutu wasu kuma su ka ji rauni bayan da aka yi fashi a wasu bankuna akalla 5 kwanaki.

KU KARANTA: Rigimar mu da Buhari ba za ta kare ba - Bukola Saraki

Babban ‘Dan Majalisar ya nemi Gwamnatin Tarayya ta kara kokari wajen kare rayukan jama’a ya kuma nemi a zauna lafiya a kasar nan. Kwankwaso yace ya kamata Jami’an tsaro su kama wadanda su kayi wannan aika-aika a makon da ya wuce.

Kafin dai bayanin Sanatan na Jihar Kano inda yace a nemo wadanda su kayi wannan abu a hukunta su, Rundunar ‘Yan Sanda ta bayyana cewa an fara kama wadanda ake zargi da laifin wannan barna da aka yi a Ranar Alhamis din da ta gabata.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel