Nigerian news All categories All tags
Buhari zai kama hanyar birnin Landan a ranar Litinin

Buhari zai kama hanyar birnin Landan a ranar Litinin

Da sanadin rahotanni na shafin jaridar Premium Times da ta kalato daga kakakin shugaban kasa Mallam Garba Shehu, shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kama hanyar sa ta zuwa birnin Landan daga garin Abuja a ranar Litinin ta gobe.

Buhari zai kama hanyar birnin Landan a ranar Litinin

Buhari zai kama hanyar birnin Landan a ranar Litinin

Mallam Shehu yake cewa, shugaba Buhari zai yi wannan ziyarar aiki ne domin ganawa da Firai Ministar kasar Birtaniya Theresa May, kan batutuwan dangartakar dake tsakanin kashen biyu a sakamakon gabatowar taron shugabannin kasashen da kasar ta 'yantar da za a gudanar a ranar 18 zuwa 20 na watan Afrilu.

Shugaba Buhari zai kuma gana da babban jami'in kamfanin Royal Dutch Plc, Mista Ben van Beurden dake da alaka da kamfanin Shell da sauran abokan hulda sakamakon shirin Najeriya na sanya hannun jari na $15bn a harkokin kasuwanci na man fetur.

Legit.ng ta fahimci cewa, wannan hannun jari zai assasa wani tushe na tsawon shekaru 20 da zai samar da makamashin iskar gas tare da habaka tattalin arzikin kasashen biyu.

KARANTA KUMA: Jam'iyyar APC reshen jihar Edo ta tubure akan tsawaita wa'adin Oyegun

Kakakin ya kara da cewa, shugaba Buhari zai kuma gana da babban limamin Cocin Canterbury, Justin Welby, wanda ya kasance na hannun daman shugaban kasa da za su tattauna akan dabbaka zaman lafiya a tsakanin addinai a kasar na Najeriya da kuma duniya baki daya.

Jaridar ta kuma ruwaito cewa, shugaba Buhari zai kuma gana da wasu fitattun mutane 'yan kasar Birtaniya da kuma na Najeriya dake zaune a can.

Sai dai kakakin bai bayyana wata alama ba ta cewa shugaba Buhari zai ziyarci Likitocin sa na birnin Landan, inda ya sha fama da jinya har ta tsawon watanni a shekarar da ta gabata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel