Nigerian news All categories All tags
Wasu 'yan ta'adda sun kashe Matafiya 10 a jihar Benuwe

Wasu 'yan ta'adda sun kashe Matafiya 10 a jihar Benuwe

Rahotanni da sanadin jaridar Daily Trust sun bayyana cewa 'yan ta'adda sun katse hanzarin wasu matafiya 10 inda suka raba su da rayuwar su a garin Yelwata dake gabar jihar Benuwe da Nasarawa akan babbar hanyar birnin Lafiya zuwa Makurdi.

Shugaban kungiyar makiyaya ta Miyetti-Allah reshen Arewa ta tsakiya, Danladi Chiroma, shine ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai na jaridar ta Daily Trust.

Danladi yake cewa, makiyaya da yammacin ranar Asabar sun gamu da ajali akan hanyar su daga garin Awe na jihar Nasarawa domin halartar wani bikin suna.

A yayin da direban wannan mota da matafiyan ke safara a cikin ke kokarin gyara sakamakon wata 'yar matsala da ta sanya suka tsahirta a daidai garin Yelwata, maharan suka bude mu su wuta, inda suka shekar da rayukan mutane goma.

KARANTA KUMA: Tsaffin gwamnoni 2 dake muradin kujerar shugaban jam'iyyar APC

Shugaban kungiyar ya ci gaba da cewa, a halin yanzu an tsinto gawawwaki 6 cikin 10 da suka riga mu gidan gaskiya kuma an mika su ga hannun hukumar 'yan sanda, inda cikin sa'a da tserar kwana direban ya shallake rijiya da baya.

A yayin haka kuma, gwamnan jihar Samuel Ortom, yayi Allah wadai da wannan hari da ya afku akan matafiya da ba su ji ba kuma ba su gani ba.

Gwamnan da sanadin sakataren sa na sadarwa Terver Akase, ya kuma yabawa jami'an tsaron na 'yan sanda da suka yi azamar cafke wadansu daga cikin wadanda suka aikata wannan aika-aika.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel