Nigerian news All categories All tags
Abinda nake son Buhari ya yiwa masu cin hanci a Najeriya - Oshiomhole

Abinda nake son Buhari ya yiwa masu cin hanci a Najeriya - Oshiomhole

Yayin da yake jawabi ga manema labarai a birnin Benin dake jihar Edo a yau, tsohon gwamna Oshiomhole, ya bayyana irin barnatar da kudin Najeriya da aka yi a mulkin PDP a matsayin rashin imani da rashin tausayi.

Oshiomhole ya bukaci shugaba Buhari ya saka takalmi karfe ya taka duk wanda aka samu da badakalar cin hanci da rashawa a kasar nan.

Tsohon gwamnan ya bayyana cewar 'yan Najeriya na bukatar sanin irin barnar da aka yiwa tattalin arzikin kasa lokacin mulkin PDP.

Buhari da Oshiomhole

Buhari da Oshiomhole

"Ni korafina ga gwamnatin tarayya shine ta dauki matakan rashin tausaya duk wadanda suka saci dukiyar kasa. Bai kamata a sassauta masu ba," inji Oshiomhole.

Sannan ya kara da cewar, "lokacin da ina gwamnati na taba bayyana cewar an saci makudan dalolin daga asusun gwamnatin tarayya, amma sai aka biya wasu masu rubutu su yi min raddin yadda a kai na san an saci kudin."

DUBA WANNAN: Hotunan dawowar shugaba Buhari Abuja bayan ziyarar da ya kai jihar Katsina

Kazalika, Oshiomhole, ya ce bai kamata jam'iyyar PDP ma tayi korafi a kan amincewa da kashe dala biliyan $1 a kan harkar tsaro da shugaba Buhari ya yi ba domin a lokacin mulkinsu sun kashe fiye da wannan adadin ba tare da amincewar majalisa ba kuma ba tare da kashe kudin ta hanyar da ya dace ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel