Nigerian news All categories All tags
Hotunan dawowar shugaba Buhari Abuja bayan ziyarar da ya kai jihar Katsina

Hotunan dawowar shugaba Buhari Abuja bayan ziyarar da ya kai jihar Katsina

Da ranar yau ne, Lahadi, shugaba Buhari ya dawo birnin tarayya Abuja bayan ziyarar da ya kai jihar sa ta haihuwa, Katsina.

Manyan jami'an gwamnati da suka hada shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin tarayya, Abba Kyari, Ministan Abuja, Mallam Mohammed Musa Bello, da shugaban hukumar 'yan sanda na kasa, Ibrahim Idris, ne suka tari shugaba Buhari yayin saukar ta sa.

Hotunan dawowar shugaba Buhari Abuja bayan ziyarar da ya kai jihar Katsina

Tasowar shugaba Buhari daga Katsina

Hotunan dawowar shugaba Buhari Abuja bayan ziyarar da ya kai jihar Katsina

Tasowar shugaba Buhari daga jihar Katsina

A wani labarin na Legit.ng, kun karanta cewar gwamnan Bauchi Ya Dawo Nijeriya Bayan Ziyarar Aiki Na kwanaki Bakwai A Kasar Amurka.

DUBA WANNAN: Buhari ya yi gaban kansa ne kawi a batun fitar da biliyan $1bn - Saraki

Gwamnan jihar Bauchi Barista Mohammed A. Abubakar, ya dawo gida Nijeriya bayan shafe mako guda a wata ziyarar aiki da ya kai kasar Amurka.

Hotunan dawowar shugaba Buhari Abuja bayan ziyarar da ya kai jihar Katsina

Dawowar shugaba Buhari Abuja bayan ziyarar da ya kai jihar Katsina

Ziyarar wadda ta kunshi taron hukumar tsaron nan na kasa da kasa wato Universal Peace Federation na majalisan dinkin duniya ta shirya.

Da yake jawabi ga manema labarai bayan dawowar sa gida Nijeriya, Gwamna M.A Abubakar, ya ce ya samu gayyata ne daga wannan hukuma ta UPF, inda suka tautauna akan matsalolin harkar tsaro da tattalin arziki a yankin Arewa maso gabashin Nijeriya da ma jihar Bauchi baki daya.

Hotunan dawowar shugaba Buhari Abuja bayan ziyarar da ya kai jihar Katsina

Dawowar shugaba Buhari Abuja bayan ziyarar da ya kai jihar Katsina

Hotunan dawowar shugaba Buhari Abuja bayan ziyarar da ya kai jihar Katsina

Dawowar shugaba Buhari Abuja bayan ziyarar da ya kai jihar Katsina

A ranar Juma'a da ta gabata ne shugaba Buhari ya isa jihar Katsina domin yin ta'aziyya ga iyalan Sanatan jihar Katsina, Mustapha Bukar, da Allah ya yiwa rasuwa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel