Nigerian news All categories All tags
Gwamnan Bauchi ya dawo Najeriya, ya zayyana abubuwan da ya koyo a ziyarar kwana bakwai a kasar Amurka

Gwamnan Bauchi ya dawo Najeriya, ya zayyana abubuwan da ya koyo a ziyarar kwana bakwai a kasar Amurka

Gwamnan jihar Bauchi Barista Mohammed A. Abubakar, ya dawo gida Najeriya bayan shafe mako guda a wata ziyarar aiki da ya kai kasar Amurka.

Ziyarar wadda ta hada da taron hukumar tsaro ta kasa da kasa wato Universal Peace Federation da majalisan dinkin duniya (MDD) ta shirya.

Da yake jawabi ga manema labarai bayan dawowar ta sa gida Nijeriya, Gwamna Abubakar, ya ce ya samu gayyata ne daga hukumar ta UPF, inda suka tautauna akan matsalolin harkar tsaro da tattalin arziki a yankin Arewa maso gabashin Nijeriya da jihar Bauchi baki daya.

Gwamnan Bauchi ya dawo Najeriya, ya zayyana abubuwan da ya koyo a ziyarar kwana bakwai a kasar Amurka

Gwamnan Bauchi ya dawo Najeriya, ya zayyana abubuwan da ya koyo a ziyarar kwana bakwai a kasar Amurka

A wani bangare ziyarar, Gwamna Abubakar, ya halarci taron zaman lafiya da tattalin arziki a jami'ar Grandview University, wanda dan asalin jihar daga karamar hukumar Bogoro mai suna Farfesa Amadu Baba Singhri ya shirya.

DUBA WANNAN: Dumu-dumu: An kama wasu matasa suna sata a wani gida a Kano, duba hotunansu

Gwamna Abubakar ya bayyana cewar ya koyo abubuwa da dama a ziyara da tarukan da ya halarta taron a kan tsaro, inda ya ce ya koyi yadda za a inganta tsaron kasa, haka kuma wannan ziyara ya kara fadada ilimi akan harkokin tsaro na jihar Bauchi.

Hukumar ta 'Universal Peace Federation', hukuma ce ta kasa da kasa wadda ba ruwan ta da addini, kungiya ce mai wakilci daga bangarori daban-daban da suka hada da masu zaman kansu da kungiyoyi. Inda Babban burin wannan kungiya shine samar da zaman lafiya a duniya baki daya.

Wannan bayani ya fito ne daga mai tallafawa a kan sadarwa Alh. Shamsuddeen Lukman Abubakar, kamar yadda Rariya ta wallafa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel