Nigerian news All categories All tags
Sai da hadin kai Sanatoci da Shugaba Buhari za su zauna lafiya kalau inji Saraki

Sai da hadin kai Sanatoci da Shugaba Buhari za su zauna lafiya kalau inji Saraki

- Bukola Saraki ya nemi a hada kai tsakanin bangaren Shugaban kasa da Majalisa

- Shugaban Majalisar yace idan babu wannan ba za a taba samun zaman lafiya ba

- Saraki yace akwai bukatar ‘Yan Majalisa su rika shiga harkar kasafin kudin kasar

Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki ya bayyana cewa rikicin sa da Fadar Shugaban kasa da sauran masu rike da madafin iko ba zai kare ba har sai an samu hadin-kai da tuntubar juna a tsakanin su domin abin ba gasa bane.

Sai da hadin kai Sanatoci da Shugaba Buhari za su tafi lafiya kalau inji Saraki

Dole Gwamnatin Buhari ta rika tuntubar mu inji Saraki

Bukola Saraki yayi magana ne game da matsalar da ake samu wajen kasafin kudi da kuma tantance wasu da Shugaban kasar ya zaba ya ba mukami inda yace ko wanene ke rike da Majalisar ba za a zauna lafiya ba sai an samu hadin-kai.

KU KARANTA: Shugaban kasa Buhari ya koma biyan tallafin man fetur

A cewar Bukola Saraki, ya kamata ‘Yan Majalisa su rika shiga harkar shirya kasafin kudi ba kurum sai an kammala aikin ba sai a kawowa Majalisa kundin. Saraki ya nemi a canza tsarin da ake tafiya a kai idan ana neman zaman lafiya.

Shugaban Sanatocin kasar ya bayyana wannan ne lokacin da ya je Jihar Filato yace idan har ba a gyara ba to babu yadda za ayi a amincewa da kasafin kudi cikin watanni 4 don haka ya nemi Shugaban kasa da Majalisa su rika aiki tare.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel