Nigerian news All categories All tags
An fara shirin koro Sanata Dino Melaye daga Majalisar Dattawa

An fara shirin koro Sanata Dino Melaye daga Majalisar Dattawa

Mun samu labari cewa Hukumar zabe na kasa watau INEC ta fara yunkurin dawo da Sanatan Yammacin Jihar Kogi Sanata Dino Melaye gida bayan da maganar ta lafa inda shi kuma ya ruga Kotun koli na kasar.

INEC ta dawo da maganar yi wa Sanata Dino Melaye kiranye inda ta sa ranar karbar sa-hannu daga mutanen da yake wakilta wanda sun haura 188, 000. Ana kukan cewa Sanatan ba ya aikin da aka tura sa a Majalisar Dattawan kasar.

An fara shirin koro Sanata Dino Melaye daga Majalisar Dattawa

An dawo da maganar yi wa Sanata Dino Melaye kiranye gadan-gadan

Tun kwanakin baya dai aka fara shirin maido Sanatan gida sai dai don dole aka dakatar saboda wani hukunci da Kotu ta yanke da farko kafin ta bada umarni Hukumar zabe ta cigaba da aikin ta. Yanzu dai maganar ta dawo.

KU KARANTA: Abin da ya hana Buhari kama su Obasanjo da Jonathan

An sa zuwa karshen wannan watan a matsayin lokacin da za a karasa tantance masu zaben raba-gardamar kiranyen. Wasu dai na cewa ya kamata Sanatan ya dawo gida yayin da wasu ke cewa yana yi masu aiki a Majalisa.

Shi dai Sanatan ya garzaya babban Kotun Najeriya a Birnin Tarayya inda yake kalubalantar yunkurin. Dama dai can Sanata Dino Melaye ya cika baki cewa babu wanda ya isa ya hana shi karasa wa’adin sa a Majalisar Dattawan kasar

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel