Nigerian news All categories All tags
Buhari ya yi gaban kansa ne kawi a batun fitar da biliyan $1bn - Saraki

Buhari ya yi gaban kansa ne kawi a batun fitar da biliyan $1bn - Saraki

A jiya ne shugaban majalisar dattijai, Sanata Abubakar Bukola Saraki, ya bayyanawa duniya cewar shugaba Buhari bai tuntubi shugabancin majalisun tarayya ba kafin ya amince da fitar da dala biliyan $1bn daga asusun kasa domin sayen kayan aiki ga hukumar sojin Najeriya ba.

A satin da ya gabata ne, Ministan tsaro, Mansur Dan-Ali, ya bayyana cewar, shugaba Buhari, ya amince da sayen kayan aiki ga hukumar sojin Najeriya da adadin kudinsu ya kai Dala biliyan $1bn.

Da yake jawabi jiya a wajen wani taro a Jos, jihar Filato, Saraki, ya ce bangaren zartarwa ba zai iya mulkin Najeriya shi kadai ba domin a tsari na siyasa dole bangarorin zartarwa da na majalisa su yi aiki tare domin kawo cigaban kasa.

Buhari ya yi gaban kansa ne kawi a batun fitar da biliyan $1bn - Saraki

Buhari da Saraki a wata ganawar su

Kazalika, Saraki, ya alakanta jinkirin zartar da kasafin kudin shekarar nan da kalubalen tsaro da kasar nan ke fuskanta da kuma gujewa samun takun saka tsakanin bangaren majalisa da na zartarwa.

DUBA WANNAN: Hotuna daga taron gangamin jam'iyyar PDP a jihar Katsina

Saraki ya yi watsi da batun cewar ana samun sabani tsakanin majalisa da bangaren zartarwar ne saboda banbancin jam'iyya tare da bayyana cewar ko a lokacin mulkin Jonathan da PDP keda rinjaye a majalisun tarayya an samu sabanin fahimta a kan abubuwa da dama tare da bayyana cewar matsalar a kan yadda za a tafiyar da harkokin gwamnati ne ba na siyasa ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel