Nigerian news All categories All tags
Dole-uwar-naki: Jami'in majalisar dinkin duniya ya yabawa shugaba Buhari

Dole-uwar-naki: Jami'in majalisar dinkin duniya ya yabawa shugaba Buhari

Babban jakada na dindindin a majalisar dinkin duniya Ambasada Samson Itegboje da ke wakiltar kasar Najeriya a majalisar ya bayyana cewa tabbas fa shugaba Muhammadu Buhari ya daga martabar Najeriya cikin shekaru 3 na mulkin sa duk kuwa da kalubalen da yake fuskanta.

Ambasada Samson Itegboje ya bayyana hakan ne a yayin wani taron tattaunawa da majalisar ta dinkin duniya a karkashin ofishin sa ta shiryawa 'yan Najeriya mazauna kasashen waje.

Dole-uwar-naki: Jami'in majalisar dinkin duniya ya yabawa shugaba Buhari

Dole-uwar-naki: Jami'in majalisar dinkin duniya ya yabawa shugaba Buhari

KU KARANTA: Magu yayi wa 'yan Najeriya muhimmin alkawari

Legit.ng ta samu cewa Ambasada Samson Itegboje ya kara da cewa tabbas wasu nasarorin ma da gwamnatin ta samu har yanzu al'ummar kasar ba ta gama sanin su ba ma.

A wani labarin kuma, Uwar kungiyar daukacin al'ummar Najeriya mabiya addinin Kirista watau Christian Association of Nigeria (CAN) sun nesanta kansu da kungun wasu fastoci 'yan asalin arewacin Najeriya da suka ziyarci shugaba Muhammadu Buhari a fadar sa satin da ya gabata.

Kungiyar dai idan mai karatu bai manta a satin da ya gabata ta kai wa shugaba Buhari ziyarar ban girma a ofishin sa inda har ma suka jaddada mubayi'ar su gareshi tare da cewa sun amince cewar shugaban baya nuna banbanci tsakanin addinan kasar.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel