Nigerian news All categories All tags
2019: Saraki sai ya fuskanci fushin Ubangiji muddin bai tsaya takara ba - Inji wani malamin addini

2019: Saraki sai ya fuskanci fushin Ubangiji muddin bai tsaya takara ba - Inji wani malamin addini

Wani babban malami kuma limamin addinin Kirista dake zaune a jihar Legas, Manzo Elijah Ayodele, ya roki shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki, akan ya nemi tsayawa takarar kujera ta shugaban kasa a zaben 2019 mai gabatowa.

Limamin ya yi gargadin cewa akwai mummunan sakamako ga tsohon gwamnan jihar Kwara muddin ya ki neman takarar shugaban kasa a kakar zabe ta shekara mai gabatowa.

Shugaban majalisar dattawa; Bukola Saraki

Shugaban majalisar dattawa; Bukola Saraki

Ayodele wanda shine babban limamin Cocin Inri Evangelical ya bayyana hakan a makon da ya gabata yayin sadaukar da wani dakin taro na zamani da ya yi a unguwar Isheri-Olofin ta jihar Legas.

KARANTA KUMA: Ina kaunar mata ta, amma ba zan iya ci gaba da zama da ita ba - Wani magidanci ya shaidawa Kotu

Yake cewa, "Ubangiji ya na son ya yi amfani da Saraki wajen taka wata muhimmiyar rawa a kasar nan domin daidaiton wasu ababe da suka kauce daga turbar tsari. Saboda haka Saraki ba ya da wani zabi face na tsayawa takara."

Ya kara da cewa, "muddin ya yi rashin biyayya dangane da wannan lamari to ko shakka ba bu sai fuskanci fushi da azabar Ubangiji."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel