Nigerian news All categories All tags
Yaki da rashawa: Shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu ya yi wa 'yan Najeriya sabon alkawari

Yaki da rashawa: Shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu ya yi wa 'yan Najeriya sabon alkawari

Shugaban hukumar nan dake yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau Economic and Financial Crimes Commission (EFCC) a takaice mai suna Ibrahim Magu ya yi wa 'yan Najeriya alkawarin cewa hukumar sa sai ta ga bayan cin hanci da rashawa.

Mista Ibrahim Magu dai yayi wannan alkawarin ne a yayin da yake fira da 'yan jarida a garin Abuja babban birnin tarayya yayin wani taron karawa juna sani da aka shirya wa wasu daga cikin mukarraban gwamnatin tarayya.

Yaki da rashawa: Shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu ya yi wa 'yan Najeriya sabon alkawari

Yaki da rashawa: Shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu ya yi wa 'yan Najeriya sabon alkawari

KU KARANTA: Kawunan yan kungiyar CAN sun rarraba kan Buhari

Legit.ng ta samu cewa dai ya kuma bayyana cewa tabbas hukumar tana kokari amma fa ya zama dole ne su sake zage dantsen su sannan kuma babu wanda ya isa ya hana su gudanar da aikin su tare da kawar da dukkan wani barbashin cin hanci da rashawa a kasar.

A wani labarin kuma, A cikin wani sako da ya aike ta asusun sa na dandalin sadarwar zamani ta Tuwita, tsohon gwamnan Gombe dake a shiyyar arewa ta gabas kuma Sanata mai wakiltar jihar a majalisar dattijai Sanata Danjuma Goje yayi kaca-kaca da tsarin nan na tallafawa gajiyayyu da masu karamin karfi tare da matasa na gwamnatin nan ta shugaba Buhari na N-power.

Wannan dai na kunshe a cikin wajen sakonnan da ya rubuta a asusun na sa a ranar Juma'ar da ta gaba inda ya koka akan yadda yace al'ummar mazabar sa sam basu anfana da shirin yadda ya kamata.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel