Nigerian news All categories All tags
Dalilin da yasa Buhari ya kasa kama Obasanjo da Jonathan - Farfesa Sagay

Dalilin da yasa Buhari ya kasa kama Obasanjo da Jonathan - Farfesa Sagay

Shugaban kwamitin tattaunawa da shawarwari game da yadda za'a kawo karshen cin hanci da rashawa wanda shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya kafa watau Farfesa Sagay ya bayyana dalilan da yasa har yanzu tsaffin shugabannin Najeriya Obasanjo da Jonathan suka gagara kamawa.

Mista Farfesa Sagay ya bayyana hakan ne a yayin firar da yayi da manema labarai biyo bayan matsin lambar da gwamnatin ke samu daga 'yan Najeriya na bukatar kama tsaffin shugabannin.

Dalilin da yasa Buhari ya kasa kama Obasanjo da Jonathan - Farfesa Sagay

Dalilin da yasa Buhari ya kasa kama Obasanjo da Jonathan - Farfesa Sagay

KU KARANTA: Wani matashi ya yi ridda a Arewa

Legit.ng ta samu dai cewa Farfesa Sagay ya ce babban dalilin rashin kama su din shine cewar har yanzu siyasar mu ta ta yi girman da hakan zai iya faruwa ba kamar sauran kasashen duniya kuma hakan zai iya jawo rikici da tashin hankali cikin kasa.

A wani labarin kuma, Tsohon gwamnan jihar Sokoto kuma daya daga cikin jiga-jigan babbar jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) Alhaji Attahiru Bafarawa ya bukaci daukacin 'ya'yan jam'iyyar da su koma ma Allah tare da rokon gafarar zunuban da suka aikata domin sune dalilin kubucewar mulki daga hannun su.

Alhaji Attahiru Bafarawa yayi wannan kiran ne ga dubban magoya bayan jam'iyyar da suka halarci taron ta na shiyyar Arewa ta yamma da ya gudana a garin Katsina jiya.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel