Nigerian news All categories All tags
Sabbin bayanai sun kara bayyana game da fashin bankuna 5 da aka yi a garin Offa

Sabbin bayanai sun kara bayyana game da fashin bankuna 5 da aka yi a garin Offa

Shugaban 'yan bangar garin Offa, jihar Kwara dake a shiyyar arewa ta tsakiya mai suna Wasi'u Adepoju ya bayyana cewa jami'an sa sai da suka kirga akalla gawawwaki 50 jim kadan bayan kazamin harin da 'yan fashi suka kai a garin satin da ya gabata a bankuna.

Shi kuwa kwamishinan 'yan sandan jihar Mista Lawal Ado cewa yayi mutane 17 ne kadai suka rasa ran su ciki kuwa hadda 'yan sanda 9 da kuma farar hula 8.

Sabbin bayanai sun kara bayyana game da fashin bankuna 5 da aka yi a garin Offa

Sabbin bayanai sun kara bayyana game da fashin bankuna 5 da aka yi a garin Offa

KU KARANTA: APC tayi babban rashi dan majalisa zuwa PDP

Legit.ng dai ta samu cewa a ranar Alhamis din da ta gabata ne dai 'yan fashi suka fasa bankuna 5 da suka hada da Union Bank, Ecobank, Guaranty Trust Bank, First Bank, Zenith Bank da kuma Ibolo Micro Finance Bank.

A wani labarin kuma, Babban jakada na dindindin a majalisar dinkin duniya Ambasada Samson Itegboje da ke wakiltar kasar Najeriya a majalisar ya bayyana cewa tabbas fa shugaba Muhammadu Buhari ya daga martabar Najeriya cikin shekaru 3 na mulkin sa duk kuwa da kalubalen da yake fuskanta.

Ambasada Samson Itegboje ya bayyana hakan ne a yayin wani taron tattaunawa da majalisar ta dinkin duniya a karkashin ofishin sa ta shiryawa 'yan Najeriya mazauna kasashen waje.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel